An kama matar dake safarar yan mata domin karuwanci a kasashen waje

An kama matar dake safarar yan mata domin karuwanci a kasashen waje

Hukumar kula da shige da fice ta kasa, NIS, ta sanar da kama wata mata da ta shahara wajen safarar yan mata zuwa kasashen waje domin sana’ar karuwanci, a kan iyakar Najeriya da kasar Bini.

Rahoton jaridar Daily Nigerian ta ruwaito kwamandan NIS dake Seme, Joshua Ajisafe ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba a jahar Legas, inda yace matar ta saba yaudarar yan mata tana kaisu kasar Bini da sunan sama musu aikin yi, amma sai su buge da karuwanci.

KU KARANTA: Ya kamata Atiku da PDP su rungumi kaddara - Sanata Ahmad Lawan

“A ranar 16 ga watan Oktoba ne jami’anmu dake shiyyar Seme suka kama wasu mata uku da aka dauko daga jahar Kaduna, bayan gudanar da bincike mun gano yan matan Najeriya, wanda aka yi safararsu.

“Sun tsere daga hannun masu garkuwa dasu, kuma suna kokarin ficewa daga kasar Bini zuwa cikin Najeriya domin komawa gida, binciken ya tabbatar da cewa an yi safararsu ne daga Najeriya zuwa Cotonou domin su yi karuwanci.”

Jami’in yace a duk lokacin da yaran suka yi kokarin tserewa daga wajenta, sai ta bukaci su biyata kudin da kashe musu, idan kuma suka nemi su kaita kara ga jami’an tsaro sai ta yanke musu gashing aba, gashin hammata da kumba, ta yi barazanar za ta haukatar dasu da tsafi.

“Daga nan kuma sai ta amince da bukatarta na yin karuwanci da bauta, sa’annan sai ta yi musu alkawarin kyalesu su tafi gida da zarar sun gama biyanta wasu makudan kudade ta hanyar karuwanci."Inji shi.

Daga karshe kwamandan yace sakamakon aikin da suka yi tare da Yansandan kasar Bini sun samu nasarar kama matar, kuma sun mikata ga hukumar yaki da safara da bautar da mutane, NAPTIP domin daukan matakin daya dace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel