JAMB Ta Saki Bayanan Dalibin da Ya Fi Kowa Samun Maki a Jarabawar UTME 2025

JAMB Ta Saki Bayanan Dalibin da Ya Fi Kowa Samun Maki a Jarabawar UTME 2025

  • JAMB ta sanar da cewa Okeke Chinedu Christian ne ya fi kowa maki a UTME 2025 da maki 375, inda ya zaɓi injiniyanci a UNILAG
  • Sai dai, JAMB ta gano cewa Okeke ya riga ya shiga jami'ar Nijeriya, Nsukka, a sashin likitanci tun shekaru huɗu da suka wuce
  • Shugaban JAMB ya ce hukumar ta aika wa majalisar likitoci buƙatar haramtawa Okeke yin aikin likitanci a irin wannan yanayi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i (JAMB) ta bayyana sunayen ɗaliban da suka fi kowa samun maki a jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME) ta 2025.

Shugaban JAMB, Farfesa Ish-aq Oloyede, ya ce Okeke Chinedu Christian daga jihar Anambra ne ya fi kowa maki da maki 375 cikin maki 400 da ake nema.

Kara karanta wannan

'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa

Hukumar JAMB ta saki bayanan Okeke Chinedu Christian, dalibin da ya fi kowa maki a UTME 2025.
Daliban Najeriya na zana jarabawar shiga manyan makarantu UTME. Hoto: @JAMBHQ
Source: Facebook

Farfesa Ish-aq Oloyede, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron tsare-tsare na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja,a ranar Talata, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Arewa 2 sun samu maki mai yawa a JAMB

Ya bayyana cewa ɗalibin da ya fi samun maki ya zaɓi jami'ar Lagos a matsayin zaɓinsa na farko, don karantar Mechanical Engineering.

JAMB ta ce Ayuba Simon-Peter John daga jihar Gombe wanda ya samu maki 374 ne yake bin bayan Okeke Christian.

An rahoto cewa Ayuba ya zaɓi jami'ar Afe Babalola (ABUAD) a matsayin zaɓinsa na farko don ya karanci Mechanical Engineering.

A matsayi na uku akwai Jimoh Abdulmalik Olayinka daga jihar Kwara wanda ya samu maki 373 tare zabar jami'ar Lagos (UNILAG) a matsayin zaɓinsa na farko.

Kamar dai ɗaliban biyu na farko, Olayinka ma ya zaɓi Mechanical Engineering a matsayin darasinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu na kan siraɗi da tsohon shugaban kwamitin sulhu na PDP ya haɗe da Atiku a ADC

Sabani kan bayanan Okeke Chinedu Christian

Sai dai, a ranar Talata, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce hukumar JAMB ta gano wasu sabani game da Okeke Christian, wanda ya zama dalibi mafi maki a jarabawar UTME 2025.

Hukumar JAMB ta gano matsala a tattare da dalibin da ya fi kowa samun mafin UTME 2025
Shugaban JAMB ya ce hukumar ta nemi a hana dalibin da ya fi kowa cin UTME 2025 damar yin aikin likitanci. Hoto: @JAMBHQ
Source: Facebook

A cewar Farfesa Oloyede, bayanai daga JAMB sun nuna cewa an Okeke ya riga ya shiga jami'ar Nigeria da ke Nsukka, a sashin likitanci tun shekaru huɗu da suka gabata.

Farfesa Oloyede ya bayyana cewa JAMB ta aikawa UNN takardar don neman bayani game da ɗalibin, kuma jami'ar ta fada mata cewa Okeke yana kan yin karatu a yanzu.

Da wannan bayanin, Farfesa Oloyede ya jaddada cewa hukumar ta aika bukata ga majalisar likitoci da lula da kaƙora ta Najeriya domin tabbatar da cewa ba a bar Okeke ya yi aikin likitanci a irin wannan yanayi ba.

Abin da ya jawo dalibai suka fadi JAMB 2025

Tun da fari, mun ruwaito cewa, fiye da dalibai miliyan ɗaya da rabi sun gaza samun maki 200 a jarrabawar UTME ta 2025, sakamakon kura-kurai da hukumar JAMB ta ce ta gano.

Kara karanta wannan

Bayan murabus ɗin Ganduje, tsohon gwamna ya ce umarnin Tinubu yake jira

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya amsa cewa sakacin hukumar ne ya haddasa wannan koma baya, inda ya ɗauki alhakin matsalolin da suka shafi sakamakon daliban.

JAMB ta bayyana cewa fiye da dalibai 380,000 za su sake jarrabawar, tare da haɗa kai da ƙwararru don nazari da warware matsalolin da aka fuskanta a jarrabawar bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com