Yadda 'Aron Hannu' Ya Jawo Mummunan Hadari a Kano, Mutum 21 Sun Rasu nan Take

Yadda 'Aron Hannu' Ya Jawo Mummunan Hadari a Kano, Mutum 21 Sun Rasu nan Take

  • Wata mota kirar Toyota Hiace da babbar mota kirar DAF sun yi taho mu gama bayan daya daga cikunsu ya yi aron hannu a jihar Kano
  • Lamarin ya yi muni matuka, inda ya jawo asarar rayukan mutum akalla 21 tun kafin a bar Dakatsalle da hadarin ya afku a ranar Lahadi
  • Hukumar FRSC ta sha alwashin gudanar da cikakken bincike, tare da jan hankalin jama'a su kiyaye dokokin hanya don kare rayuka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar wasu bayin Allah sakamakon mummunan haɗarin mota da ya faru a ranar Lahadi, 6 ga Yuli, 2025.

Hadarin ya faru ne a kasuwar Dogo da ke Dakatsalle, a kan babban titin Zariya-Kano, inda aka tabbatar da mutuwar mutum 21 nan take.

Kara karanta wannan

Makircin Bello Turji na neman shirya sulhu da gwamnati ya fito fili

An yi mummunan hadari a Kano
FRSC ta tabbatar da mummunan hadari a Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

NTA ta wallafa cewa babbar motar nan da aka sani da DAF da kuma wata motar haya kirar Toyota Hiace sun yi taho mu gama da juna a kan titin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’in FRSC ya bayyana yadda hadarin ya faru

A karin bayani ta sakon murya da ya yiwa Legit ta WhatsApp, jami’in hulɗa da jama’a na FRSC a Kano, CRC Abdullahi Labaran, ya ce hadarin ya faru ne da 8.23 na safe.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa direban motar haya kirar Toyota Hiace ne ya yi aron hannu, hakan ya haddasa taho mu gama da babbar mota da ke tahowa.

A cewar FRSC, daga cikin mutane 24 da hadarin ya rutsa da su, mutum 21 sun mutu, wanda ya haɗa da maza 19 da kuma mata biyu, sauran uku kuma sun jikkata.

Ya ce:

"Mutum uku sun samu raunuka, wanda muka kai su asibiti a Garun Mallam, yayin da muka kai gawarwakin sauran mutum 21 zuwa asibitin Nassarawa."

Kara karanta wannan

Katsina: Ƴan bindiga sun yi shigar dare, sun sace Sarki yayin wani farmaki

FRSC za ta gudanar da cikakken bincike

Shugaban FRSC na ƙasa, Shehu Mohammed, ya tabbatar da cewa hukumar za ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hadarin.

Ya kuma shawarci direbobi da sauran masu ababen hawa da su kiyaye dokokin zirga-zirga domin kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi a manyan tituna.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
Mummunan hadarin ya afku ne a Dakatsalle da ke Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Game da gawarwakin, ya ce:

"Yawancinsu sun kone matuƙa, ta yadda ba za a iya gane su ba."
"Muna jan hankalin jama'a da su guji gudun wuce sa’a da kuma amfani da hanya ba bisa ƙa’ida ba, domin irin waɗannan abubuwan su ne ke haddasa hadura."

Ya bayyana damuwarsa a kan yadda wasu masu ababen hawa ke tafiya a 'hannu aro' a manyan tituna, yana mai cewa hakan na ƙara jefa rayuka cikin haɗari.

Buharin Dala ya rasu a hanyar Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala kuma jigon siyasa a jihar Kano, Injiniya Mahmoud Sani Madakin Gini, ya rasu a hadarin mota.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tare matasa da ke dawowa daga jana'iza, hadimin gwamna ya tsira

Tsohon shugaban ya rasu ne a haɗarin mota da ya rutsa da shi a hanyar zuwa birnin tarayya Abuja, inda ya nufi kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Atiku ya ce mutuwar jigon siyasar ta girgiza shi ƙwarai, tare da muka ta'aziyya duba da cewa marigayin ya shirya kai masa ziyara a Abuja kafin aukuwar hatsarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng