Makircin Bello Turji na Neman Shirya Sulhu da Gwamnati Ya Fito Fili
- An gano cewa Bello Turji ya nuna sha’awar mika wuya amma ba saboda tuba ba, illa dai don kokarin tsira da ransa
- Ana ganin cewa kwamandan ayyukansa, Danbokolo da ya mutu a samamen DSS da 'yan sa-kai ne ya rage karfinsa
- Masana tsaro sun ce mika wuya da Bello Turji ke nema ba zai kawo karshen ta’addanci a Arewa maso Yamma ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Bidiyon da ke nuna fitaccen jagoran 'yan bindiga, Bello Turji, yana nuna niyyar ajiye makamansa da karɓar zaman lafiya, ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin ƙasar nan.
Mutane da dama sun nuna shakku kan ingancin niyyar dan ta'addan da ya ce yana neman yin sulhu da daina kashe kashe.

Source: Twitter
Sai dai binciken da Zagazola Makama ya fitar a X ya nuna cewa matakin da Turji ya ɗauka ba wai na tuba bane, illa dai wata hanya ce ta neman mafita bayan da karfinsa ya fara raguwa.

Kara karanta wannan
Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasa Danbokolo ya karya lagon Bello Turji
Rahoton ya ce kwanaki uku kafin bidiyon ya fito, Turji ya fara kokarin mika wuya bayan da dakarun haɗin guiwa na DSS da 'yan sa-kai suka kashe babban kwamandansa, Danbokolo.
Danbokolo ne aka bayyana a matsayin “jagoran yaki” na bangaren Turji, wanda ke jagorantar hare-hare, kwace da kuma kisa a yankunan Zamfara da Sokoto.
Wata majiyar tsaro ta ce:
“Gaskiyar magana ita ce, yawanci Turji magana yake yi. Danbokolo ne ke jagorantar dukkanin munanan ayyuka. Da zarar Danbokolo ya mutu, to karfin Turji ya rushe.”
Bello Turji yana rayuwa cikin fargaba
Rahoton ya ce tun bayan mutuwar Danbokolo, Turji ya shiga cikin rudani, yana neman mafita daga farmakin da dakarun Najeriya ke ci gaba da kai wa maboyarsa.
Wani bayani ya nuna cewa:
“Bayan wannan mutuwar, kungiyar Turji ta rikice. Ba su da tsari, kuma yawancin mabiyansa sun gudu. Turji yanzu yana yawo ne da kansa kamar wanda aka kora daga mulki.”
Karshen Turji zai kawo zaman lafiya?
Duk da yunkurin da Turji ke yi na sulhu, masana harkar tsaro sun ce wannan ba ya nufin cewa za a samu cikakken zaman lafiya a Arewa maso Yamma.
An bayyana cewa yunkurin gwamnati na kai farmaki bisa bayanan leƙen asiri ne ya rage karfin Turji da sauran shugabannin ta’addanci.

Source: Facebook
Sai dai tambaya da masana ke yi yanzu ita ce: Shin gwamnati za ta karɓi bukatar afuwa daga wanda ya daɗe yana addabar al’umma da kashe dubban mutane?
An kafawa Turji sharadin sulhu a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Sokoto ta yi martani kan sulhu da dan ta'adda Bello Turji ya fara nema a jihar.
Legit ta rahoto cewa Bello Turji ya fara neman sulhu ne bayan kashe abokin ta'addacinsa a wani samame da 'yan sa-kai suka kai.
Gwamnatin Sokoto ta ce idan har da gaske Bello Turji ya ke yana son sulhu, ya kamata a kalli hakan a aikace, ma'ana ya daina kashe mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
