Rikici Ya Ɓarke da Aminu Ado Bayero Ya Zo Wucewa ta Fadar Sarki Sanusi II a Kano

Rikici Ya Ɓarke da Aminu Ado Bayero Ya Zo Wucewa ta Fadar Sarki Sanusi II a Kano

  • Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun farmaki fadar sarkin Kano ta Ƙofar Kudu, inda Muhammadu Sanusi II ke zaune tare da jama'arsa
  • Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi da misalin karfe 1:00 na rana lokacin da Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ya wuce ta unguwar Ƙofar Kudu
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, wanda aka ce ƴan daban sun jefa duwatsu, sun lalata babura da wasu kayayyaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - An yi wani ɗan rikici a fadar mai martaba Sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu, inda Muhammadu Sanusi II ke zaune da jama'arsa.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya zo wucewa ta kusa da fadar Ƙofar Kudu, ranar Lahadi, 6 ga watan Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 25 ɗauke da nonon mace, ƴan sanda sun yi ƙarin bayani

Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Wasu ƴan daba sun kai hari fadar Sarkin Kano da ke unguwar Kofar Kudu Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Masani kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na X yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar wannan rikici, tare da wani kisan kai da ake zargin wata mata yar shekara 25 ta yi a jihar Kano.

Yadda aka farmaki fadar Sarki ta Ƙofar Kudu

Wannan lamari na zuwa ne yayin da rikicin sarauta tsakanin Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II, da na 15, Aminu Ado Bayero ke ƙara ɗaukar lokaci ba tare da an warware shi.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa tashin hankalin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar rana jiya Lahadi daidai lokacin da Aminu Ado Bayero ya zo wucewa ta unguwar Ƙofar Kudu, kusa da fadar Sanusi II.

Rahotanni sun ce wasu ‘yan daba da ake zargin sun shige cikin taron jama’a ne suka fara jifar wani ɓangaren fadar Sarki ta Ƙofar Kudu da duwatsu, wanda hakan ya tayar da hankula.

Kara karanta wannan

Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya

An lalata kayayyaki a fadar da Sanusi ke zaune

A sakamakon haka ne aka lalata babura guda biyu tare da kuma fasa gilashin motocin ‘yan sanda guda uku da aka tura domin tabbatar da tsaro a wajen.

Jami’an tsaro sun hanzarta kai ɗauki wajen da abin ya faru, inda suka cafke mutane huɗu da ake zargi da hannu a harin.

An kai hari fadar sarkin Kano.
Yan daba sun lalata kayayyaki a fadar Sarkin Kano Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Ƴan sanda kama mutum da ake zargi

Waɗanda aka kama da hannu a jifar fadar Sarkin akwai Isyaku Uba daga unguwar Koki, Abubakar Haruna daga Daurawa, Umar Isah da Hamisu Uba, duk daga Kantudu-Dala.

Makama ya tabbatar da cewa tuni jami'an tsaro suka samu nasarar maido da doka da oda, yayin da ke ci gaba da bincike kan musabbabin harin da kuma wadanda suka shirya shi.

Rikicin saurautar Kano

Rikicin da ke ci gaba da faruwa sarki Muhammadu Sanusi II, da sarki Aminu Ado Bayero ya jefa jihar Kano cikin halin rashin tabbas da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Rashin daraja: An kama babban limamin masallaci da aukawa ƙaramar yarinya

Wannan rikici, wanda ya samo asali ne daga rushewar dokar masarautu da dawo da Sanusi II a watan Mayu 2025, ya rikide zuwa rikicin siyasa da kuma na tsaro.

Tun daga lokacin, an samu rabuwar kawuna tsakanin mabiyan sarakunan biyu, inda ko wane bangare ke kallon kansa a matsayin sahihin mai martaba.

Wannan rikici ya ƙara ta'azzara a lokacin da Aminu Ado Bayero ke ci gaba da zama a fadar Nasarawa, yayin da Sanusi II ke zaune a fadar Kofar Kudu – al’amarin da ke janyo zazzafar takaddama a tsakanin magoya bayansu.

Rikice-rikicen da ke afkuwa a kusa da fadar masarautu, kamar na baya-bayan nan da ya faru a Kofar Kudu, suna nuna yadda rikicin sarauta ke barazana ga zaman lafiya a jihar.

Hakan na ƙara bayyana gazawar hukuma wajen samar da matsaya ɗaya da kuma rashin saurin shawo kan rikicin da ke barazana ga doka da oda a jihar Kano.

Sarkin Kano ya hango matsala ga lauyoyi

A wani rahoton, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ayyukan lauyoyi na fuskantar barazana saboda zuwan fasahohin zamani kamar AI.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun daƙile mummunan shirin ƴan ta'adda, an gano bama bamai sama da 50

Sarkin ya bukaci a ƙara kwas din koyon amfani da fasahohin zamani a karatun lauyoyi na Najeriya domin inganta ayyukan masana doka a Najeriya.

Muhammadu Sanusi II, wanda aka bayan kan sarautar Kano a kwanakin baya, ya ƙara da cewa a halin yanzu, fasaha ba zaɓi ba ce ga al'umma, ta zama tilas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262