"Ku Yarda da Ni": Obi Ya Fara Lallaɓa Ƴan Arewa, Yana Neman Ƙuri'un Doke Tinubu a 2027
- Peter Obi ya roƙi 'yan Arewa su amince masa da kuri'unsu a 2027, yana mai alƙawarin kare muradunsu idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa
- Ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ƙarƙashin jam'iyyar ADC, inda ya musanta zargin zama mataimakin Atiku Abubakar
- Obi ya jaddada cewa ana buƙatar gudunmawar kowa don farfaɗo da Najeriya, gami da waɗanda suka kasance a gwamnatocin baya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – 'Dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya buƙaci manyan mutanen Arewa da talakawa daga yankin da su zabe shi a 2027.
Peter Obi, ya yi alkawarin kare muradun mutanen Arewa idan har suka amince suka ba shi ƙuri’unsu ya doke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Peter Obi ya mika kokon bararsa ga Arewa
Ɗan takarar na LP ya yi wannan kiran ne a daren Lahadi, 6 ga Yulin 2025, yayin da yake jawabi a wani shirin Channels TV mai suna 'Siyasa a Yau'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya ci gaba da cewa ya kamata 'yan Najeriya su zaɓi 'yan takara bisa ga ƙwarewarsu kowannesu ba wai ayi la'akari da yankin da suka fito ba.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce:
“Ina so Arewa ta yarda da ni. Babbar kadarar wannan ƙasa ita ce Arewa, la'akari da faɗin ƙasar. Idan ni ne shugaban ƙasa, Arewa za ta ji dadin mulkina.”
Obi zai tsaya takarar shugaban kasar 2027
Obi, wanda ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya yi watsi da rahotannin cewa zai amincewa Atiku Abubakar ya yi takarar shugaban kasa shi kuma ya zama mataimakinsa.

Kara karanta wannan
Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya
“Zan yi takarar shugabancin Najeriya. Ni mamba ne na ADC, amma babu wanda ya taɓa tattauna wa da ni a kan wai na zama mataimakin shugaban ƙasa.
"Ban san daga ina wadannan rahotannin suke fitowa ba. Ku 'yan jarida kuna hasashe a kan abubuwa da yawa ne."
- Peter Obi.

Source: Twitter
Maganar hadin kai da manyan jiga-jigan siyasa
Peter Obi ya kuma tsokaci kan sukar da wasu ke yi na cewa ya shiga jam'iyyar ADC duk da cewa ta tara kusoshin da ake zargin su ne suka jawo kasar ta koma baya.
A cewar tsohon gwamnan jihar Anambra, akwai buƙatar gudunmawar kowa da kowa don farfaɗo da Najeriya, don haka yake ganin dacewar shiga ADC.
“A zahiri, ana buƙatar waɗanda suka kasance a cikin gwamnatin da ba ta yi yi aiki ba! Ai sun san kuskuren da suka yi, kuma sun san yadda za a gyara, kuma a yanzu na tabbata kowa na son canji."
- Peter Obi.
ADC ta tura goron gayyata ga Gwamna Dauda
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban ADC na Zamfara, Kabiru Garba, ya bukaci Gwamna Dauda Lawal da ya sauya sheka zuwa jam’iyyarsu domin inganta ci gaban jihar.

Kara karanta wannan
Atiku ko Obi: Sule Lamiɗo ya fito da abin da ke ransa, ya faɗi wanda zai marawa baya a 2027
Garba ya bayyana cewa sama da mutane 100 daga jam’iyyu daban-daban sun shiga ADC, kuma tuni aka fara basu horo kan tsarin mulki da manufofin jam’iyyar.
Ya kara da cewa jam’iyyar ta bude kofa ga duk masu sha’awar sauya sheka, tare da tabbatar da daidaito da damar dimokuradiyya ga kowane memba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
