ADC Ta Yi Martani ga Fadar Shugaban Kasa, Ta ce Ta Gama Gigita APC

ADC Ta Yi Martani ga Fadar Shugaban Kasa, Ta ce Ta Gama Gigita APC

  • Jam’iyyar ADC ta ce gwamnatin APC na tafiyar da kasar nan yada ta ga dama tare da jefa jama'a a cikin yunwa da gangan
  • Zargin na zuwa bayan hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce an kammala shirin kawar da kalubalen karancin abinci
  • Sakataren rikon yada labaran ADC, Mallam Bolaji Abdullahi ya ce bullar jam'iyyarsu ce ta girgiza APC har ta fara nemo mafita

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nade hannayenta da gangan, tare da barin 'yan Najeriya a cikin mugun yanayi.

Jam'iyyar ta ce sababbin tsare-tsare, musamman a kan samar da abinci ya wadata ga talakawa ya samo asali ne daga bayyanar yan adawa a ADC.

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

ADC ta caccaki gwamnatin APC
ADC ta ce ta zaburar da gwamnatin APC Hoto: @ADCngcoalition/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Wannan na cikin wani saƙo da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na X, wanda Mallam Bolaji Abdullahi, Sakataren Yaɗa Labarai na Kasa na riko, ya sa wa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ADC ta caccaki gwamnatin APC

A cewar ADC, fargabar da ke addabar jam’iyyar APC na da nasaba da karin karbuwa da tasirinta a tsakanin jama'a tun bayan bullarta a yan kwanakin nan.

Wannan martani ne ga furucin hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, inda ya ce gwamnati na shirin cire dukkanin kalubalen da ke hana samun wadatar abinci a kasar.

Shugaban riko na ADC, David Mark
ADC ta ce gwamnatin APC ba da gaske ta ke ba Hoto: APC Coalition 2027
Source: Twitter

Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana mamakinsa kan yadda sai bayan fitowar kawancen jam’iyyun adawa ne gwamnatin Tinubu ta fara tunanin hanyoyin da za a ceto rayuwar talakawa.

Ya ce da ba don matsin lambar da fitowar kawancen adawa ya haifar ba, da gwamnati ta cigaba da nuna halin ko in kula da halin da 'yan kasa ke ciki.

Kara karanta wannan

Yobe: Hadimin gwamna ya yi murabus, ya faɗi dalilansa na shiga jam'iyyar ADC

'An bar Najeriya da yunwa,' ADC

ADC ta yi zargin cewa da gangan gwamnatin APC ke amfani da yunwa wajen ta'azzara rayuwar jama'a, wanda yake amfani da shi a matsayin makami na siyasa.

Jam'iyyar ta ce:

“Lokacin da Onanuga ya ce za su cire kalubalen da ke hana cimma burin gwamnatin Tinubu wajen wadatar abinci da fitar da shi waje, ya bayar da tabbaci ne.
Ya bayar da tabbacin cewa da gangan wannan gwamnati ta ki daukar mataki yayin da 'yan Najeriya ke cikin yunwa. Yanzu kuma, saboda matsin siyasa, suna son a yi musu jinjina? Wannan ba sauyi ba ne. Ba shugabanci ba ne. Wannan dai yunƙurin ceton kai ne daga gazawar da suka jefa kansu ciki.”

— Mallam Bolaji Abdullahi

Tsohon dan takarar gwamna ya koma ADC

A baya, mun ruwaito cewa Ibrahim Ali Amin Little, tsohon dan takarar gwamnan Kano kuma jigo a PDP, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar bayan bullar ADC.

Kara karanta wannan

Yaƴan jagororin ADC da ke cikin jam'iyyun APC da PDP a yau

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tudun Wada dake jihar Kano yayin da ake shirin 2027.

Tsohon dan takarar ya nuna rashin jin daɗinsa kan rikicin shugabanci da ya addabi PDP a matakin jiha da na kasa, yana mai cewa hakan babbar matsaya ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng