'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Buɗe Wuta ana tsakiyar Sallah a Jihar Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Buɗe Wuta ana tsakiyar Sallah a Jihar Sakkwato

  • Ƴan bindiga sun buɗe wa mutane wuta suna tsakiyar sallar Azahar a kauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza a Sakkwato
  • Mazauna kauyen sun tabbatar da cewa maharan, waɗanda ake zaton ƴan Lakurawa ne sun kashe akalla mutane 15 a harin
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta ce ba a gama tantance adadin waɗanda suka rasa rayukansu ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Wasu ƴan bindiga da ake zaton mayaƙan kungiyar Lakurawa ne sun kashe mutum 15 a wani hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a jihar Sakkwato.

Ana ganin dai wannan hari da suka kai da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata, na ramuwar gayya ne, bayan an kashe wasu ƴan Lakurawa uku a yankin.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An kashe gawurtaccen ɗan bindiga da ya addabi al'umma a Zamfara

Lakurawa sun kashe mutum 15 a Sakkwato.
Yan bindiga sun farmaki mutane ana tsakiyar sallar Azahar a Sakkwato Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da wani da ake kyautata zaton kwamanda ne a kungiyar Lakurawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hari a Masallaci

Wani ɗan ƙauyen da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce 'yan bindigar sun mamaye garin ne a lokacin da mutanen ke cikin masallaci suna sallar Azahar.

“Muna cikin masallaci sai muka ji harbe-harbe. Sun shigo ƙauyen da yawa, suka buɗe wuta kan jama’a ba tare da kebe kowa ba, sun harbi masallata da manoma.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar Tangaza sun ziyarci ƙauyen a ranar Laraba domin halartar jana’izar waɗanda aka kashe.

“Wannan shi ne karo na farko da ƴan Lakurawa suka kawo hari ƙauyenmu. Amma ina da yakinin cewa ramuwar gayya ce bayan an kashe mutane uku daga cikinsu," in ji shi.

Ƴan Lakurawa sun lalata dukiyar jama'a

Wani mazaunin ƙauyen ya ce ‘yan bindigar sun ƙona gonaki da gidajen jama'a da dama yayin harin amma ba su taɓa mata ba.

Kara karanta wannan

Bam ya tarwatse da matafiya a Yobe, an samu asarar rayuka

“Ba su taɓa mata ba, amma sun kashe maza, sun lalata kayan abinci baki ɗaya, har da na shaguna. Sun ƙone gidajen jama'a,” in ji shi.

Bayan harin, mutane da dama sun tsere daga ƙauyen, domin neman mafaka a wasu garuruwan makwabta.

Gwamna Ahmed Aliyu na Sakkwato.
Mutum 15 sun mutu a harin ramuwar gayya da ƴan Lakurawa suka kai Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu
Source: Facebook

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba a tabbatar da adadin waɗanda aka kashe ba tukuna.

Wata majiya daga ƙaramar hukumar ta tabbatar da cewa mutum 15 ne suka mutu, yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon harbin bindiga kuma an garzaya da su asibiti.

Gwamnatin Sakkwato ta buɗe kofar sulhu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Sakkwato ta ce a shirye take ta yi sulhu da ƴan bindiga domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Mai ba gwamnan Sakkwato shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman mai ritaya ya ce ƙofar gwamnati a buɗe take don tattaunawa da ƴan bindiga.

Ya ƙara da bayyana cewa dole ne sai ‘yan bindigar da ke son a yi sulhu sun nuna cikakken niyyar ajiye makamansu, da barin ayyukan ta'addanci gaba ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262