A Karo na 2, Bam Ya Tashi da Mutane Suna tsakiyar Sauke Kaya a Jihar Kano
- Mutane sun shiga fargaba da bam ya sake tashi a kamfanin ƴan gwangwan a Kofar Dawanau da ke ƙaramar hukumar Dala a Kano
- Rahotanni sun nuna cewa mutum ɗaya ya rasa ransa, wasu shida sun samu raunuka sakamakon fashewar a ranar Litinin da ta gabata
- Wannan lamari na zuwa ne bayan tarwatsewar abin da faru a Eastern Bypass, wanda ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkata wasu 15
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ƙirar gida ya tashi a Kofar Dawanau da ke ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano da yammacin Litinin, 30 ga Yuni, 2025.
Wannan mummunar fashewa ta yi sanadin rasuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu bayin Allah har mutane shida.

Source: Original
Yadda bam ya kashe mutane a Kano
Tribune Online ta rahoto cewa wannan lamari na zuwa ne makonni bayan wani bam ya tashi a ranar 21 ga Yuni, 2025, a titin Eastern Bypass.
Lamarin ya jawo rasa rayukan mutane akalla biyar yayin da wasu 15 suka samu raunuka daban-daban.
Wannan ya kara jefa jama'a cikin fargaba dangane da yaduwar abubuwan fashewa a kasuwannin kayan bola-bola a faɗin jihar.
Kano ta ƙara fuskantar tashin bam karo na 2
Wani shaida ya bayyana cewa sabuwar fashewar ta faru ne a wurin ƴan gwangwan da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin da ta shige.
Ya ce ana zargin an shigar da wata tsohuwar nakiya (bam da ake ƙarawa a gida) cikin tarkacen karafa da ake saukewa, kuma ta tarwatse.
A binciken farko da sashen kwance bam na ‘yan sanda suka gudanar, an gano cewa bam ɗin na cikin ƙarafan da aka sauke daga wata babbar mota mai lamba PKM 709 ZY.
Mutum nawa suka rasu a fashewar Kano?
Abin takaici, wani lebura ɗan shekaru 55, Hamisu Uzairu, mazaunin unguwar PRP Kwanar Jaba a cikin karamar hukumar Nasarawa, ya rasa ransa a fashewar.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Fada ya barke tsakanin wasu 'yan gida 1 a Filato, an yi kisan kai
An tabbatar da mutuwarsa ne a Asibitin Murtala Muhammed a Kano, inda aka garzaya da shi da sauran waɗanda suka jikkata domin samun kulawa ta gaggawa.
Mutum shida da suka jikkata sun haɗa da Sani Ahmed, Najib Sani, Jabir Tijani, Wada Abdullahi, Huzaifa Yusha’u, da Bilyaminu Sani, yanzu haka suna kwance a asibiti.

Source: Twitter
Mai kamfanin na ƴan gwangwan, Jamilu Zakari Salisu, ya sanar da ‘yan sandan Dala nan take bayan fashewar bam din, lamarin da ya jawo hankalin jami’an tsaro, suka kulle wurin tare da fara bincike.
Jami'an tsaron na koƙarin gano asalin abin da ya fashe, tare da tono raguwar bama-bama idan akwai a sauran kayayyakin da aka sauke.
Sai dai har zuwa wannan lokacin, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ba ta fitar da sanarwar hukuma dangane da fashewar ba.
Tarihin tashin bam a Kano
Jihar Kano ta sha fuskantar munanan hare-haren bama-bamai a cikin shekaru goma da suka wuce, wanda ya jefa al’ummar jihar cikin fargaba a lokuta daban-daban.
Daya daga cikin manyan hare-haren da aka fi tunawa da shi shi ne na ranar 20 ga Janairu, 2012, lokacin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai hare-hare na bama-bamai da bindigogi a wuraren tsaro da cibiyoyin gwamnati.
A wannan lokaci, an tabbatar da rasuwar sama da mutane 180 – har yanzu yana daga cikin mafi muni a tarihin jihar.
A shekarar 2014, wasu bama-bamai sun tashi a tashar mota ta Sabon Gari, inda mutane da dama suka mutu.
Haka kuma, a shekarar 2015, wani harin bam ya tashi a babban masallacin Sarki yayin sallar Juma’a, inda aka rasa mutane fiye da 100.
Matashi ya hau dogon ƙarfe a Kano
A wani labarin, kun ji cewa wani matashi ya ɗare kan babban allon tallace tallace a Gadar Lado da ke hanyar Zaria a cikin birnin Kano.
Wannan al'amari dai ya ja hankalin mutane, wadanda suka kewaye wurin suna kallo tare da fargabar mutumin na iya yunƙurin faɗowa.
Ƴan sanda sun kai ɗauki tare da sauko da mutumin lami lafiya, amma sun ce da yiwuwar a hukunta shi bisa zargin yunƙuirin kisan kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

