Ku Zo Ku Siya: AMCON Ta Saka Kadarorin Gwamnati 10 a Kasuwa, Ana Neman Masu Saye
Abuja - Hukumar kula da kadarori ta Najeriya (AMCON) ta fitar da jerin kadarori 10 da za ta cefanar da su a manyan jihohi kamar Legas, Abuja, Oyo, Filato, da kuma Rivers.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan wani bangare ne na ƙoƙarin hukumar AMCON na gudanarwa da warware matsalolin kadarorin da ba su samar da wata riba, musamman waɗanda aka karba daga cibiyoyin kuɗi.

Source: Twitter
Za a sayar da kadarori 10 a jihohi 5
Wata sanarwar talla da aka wallafa a jaridar ThisDay a ranar Litinin ta yi cikakken bayani kan kadarorin da aka sanya a kasuwa da yadda za a sayar da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce kadarorin sun haɗa da gine-ginen ofisoshi na kasuwanci, gidajen zama, da kuma rumbunan ajiyar kayayyaki.
Hukumar ta bayyana cewa za a sayar da waɗannan kadarori ta hanyar tsarin gwanjo, kuma za a rufe karɓar takardun neman sayen kadarorin nan da ranar 11 ga Yuli 2025.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Fada ya barke tsakanin wasu 'yan gida 1 a Filato, an yi kisan kai
AMCON ta tabbatar da cewa za a sanar da jadawalin buɗe kofar gabatar da takardun shiga gwanjon nan ba da jimawa ba.
Wannan matakin ya biyo bayan canja shugabannin AMCON da gwamnatin tarayya ta yi kwanan nan, wanda ke da nufin inganta gudanarwa da dawo da darajar kadarorin da ba su da amfani.
Cikakken jerin kadarori 10 da za a sayar
1. Rumbun ajiya da Ofis a Ibadan, Jihar Oyo
Wannan kadara tana Km 9, titin Old Legas, Podo (Plot 1, 2 & 3 Road 1 Zone 2), Mogbojubola Layout, Opere Industrial Village.
Kadarar ta haɗa da rumbun ajiya, ofis, gidan mai gadi, bandaki na waje, da kuma gidan injin samar da wuta. Kadarar ta kai girman murabba'in mita 12,802.83.
2. Ofis a Gbagada, Legas
Wannan kadara tana a 3 Sawyer Crescent kusa da makarantar Corona. Tana dauke da ginin ofis mai hawa biyu, gidan injin samar da wuta, da kuma gidan mai gadi.
Duk da cewa an tsara ginin kadarar a matsayin gidan zama, ana iya amfani da ita a matsayin ofis ko makaranta idan an samu izinin hukuma. Girman ƙasar ya kai murabba'in mita 1,343.10.
3. Tsohon otal din Sumiram da gidan abinci a Filato
Wannan wurin yana kan Secretariat Link Road. Yana da babban gini mai ɗakuna shida, ɗakunan bayi biyu, madafa, kantin sayar da abinci, da kuma wurin tarbar baƙi.
4. Gini mai hawa 5 a Silverbird Mall, Abuja:
Wannan ginin yana a Central Area, Cadastral Zone. Yana da jimillar girman kasa na murabba'in mita 15,650.10.
Wannan kadara tana daga cikin kadarorin da AMCON ta karɓa a shekarar 2016, da ke da alaƙa da bashin Naira biliyan 11 da ake bin rukunonin kamfanin Silverbird.
5. Rumbun ajiya da Ofis a jihar Ribas
Wannan kadara tana kusa da gadar Isaac Boro Park a No. 2, Aba Road. Ya haɗa da rumbun ajiya da ofis wanda ke da girman murabba'in mita 2,529.63.

Source: UGC
6. Rukunin gidaje 6 a Rumuodara, jihar Rivers:
Wannan kadara tana a 216 Okporo Road, karamar hukumar Obi Akpor. Ta ƙunshi rukunin gidaje shida na ɗakuna uku da kuma dakin mai gadi a kan murabba'in mita 613.19 na ƙasa.

Kara karanta wannan
Ba daraja: Sarki ya zargi tsohon gwamna da wawure kason masarauta kafin barin mulki
7. Gidaje a GRA Phase 3, Port Harcourt:
Wannan wurin ya haɗa da gidaje biyu masu ɗakuna biyar, gidaje biyu masu ɗakuna huɗu, dakin mai gadi, da kuma gidan janareta, a kan fili mai girman murabba'in mita 2,360.32.
8. Gidan zama mai dakuna 5 a Rumuogba, Port Harcourt:
Wannan kadara tana a 4 Nda Street, kusa da Eliada Layout. Tana da gini mai hawa biyu mai ɗakuna biyar, ɗakin ma'aikacin gida, dakin mai gadi, da kuma gidan janareta a fili mai girman murabba'in mita 691.87.
9. Rumbunan ajiya 2 a Port Harcourt/Aba Expressway:
Kadarar tana a Km 2 Port Harcourt/Aba Expressway. Ta haɗa da rumbunan ajiya biyu da kuma dakin mai gadi. Girman filin kadarar ya kai murabba'in mita 7,607.99.
10. Gida a C & C Estate, Port Harcourt:
Wannan gini mai hawa biyu yana a Plot 8, kusa da R.D Road, kusa da Okporo Road. Ya haɗa da ɗakunan bayi, dakin mai gadi, da kuma gidan janaret, yana da girman fili na murabba'in mita 811.12.
Wannan mataki na AMCON zai taimaka wajen dawo da kuɗaɗen da bankuna suka ba da rance waɗanda ba a biya ba, tare da ba da dama ga masu saka hannun jari don mallakar kadarori a manyan wurare a Najeriya.
Gwamnati ta cefanar da kadarorin bankin Heritage
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar Inshorar Bankuna ta Najeriya (NDIC) ta fara siyar da kadarorin bankin Heritage tun daga ranar 4 ga Disamba, 2024, a duk faɗin ƙasar.
Daraktan sadarwa na NDIC, Bashir Nuhu, ya bayyana cewa kamfanoni da daidaikun mutane sun duba kadarorin kuma sun shiga cikin gwanjon sayar da su.
NDIC ta sanar da cewa za a sayar da kadarorin bankin ne a biranen Abuja, Legas, da sauran wurare, tare da ba da ƙarin bayani ga jama'a kan yadda gwanjon ya gudana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

