'Yadda kotuna zasu agazawa AMCON ta kwato basukan cikin gida da sun kai tiriliyan biyar da rabi'

'Yadda kotuna zasu agazawa AMCON ta kwato basukan cikin gida da sun kai tiriliyan biyar da rabi'

- Basukan cikin gida a yanzu sun doshi tiriliyan shidda

- Cif Joji na kasa, na so AMCON ta bi hanyoyin sulhu don kwato kudaden

- Shugaban Kasa ya sanya AMCON ta amso kudaden

'Yadda kotuna zasu agazawa AMCON ta kwato basukan bankuna da sun kai tiriliyan biyar da rabi'
'Yadda kotuna zasu agazawa AMCON ta kwato basukan bankuna da sun kai tiriliyan biyar da rabi'
Asali: Depositphotos

Tun bayan da gwamnatin Tarayya ta sha alwashi na lallai sai ta karbo ko rago maqudan kudaden da ake bi a cikin gida, hala na gwamnatoci ne, a'a na bankuna ne, ko na 'tyan kwangila da ma na kasuwanni, wanda a yanzu sun kai tiriliyan biyar da biliyan 400,000, kotuna sun cika fal da kesa-kesai na bin kadin basukan.

AMCON, a doka, ita ce hukumar da ke iya bin kadin karbo irin wadannan basussuka ko kadarori daga wadanda suka ci bashi.

A yanzu, Cif joji na kasa, Alkalin Alkalai, Jastis Walter Onnoghen, a taron kotunan da Asset Management Corporation of Nigeria (AMCON) din, an sami cimma matsaya kan yadda za'a rage bata lokaci da kumbiya-kumbiya ta kotuna kan yadda za'a rampo kudaden da kadarorin.

DUBA WANNAN: Yadda Kwankwaso zai koyi siyasa daga Tinubu

A cewar Cif Jojin, tun da kotuna basu da lokaci, basu kuma da kudaden da ake bukata na samar wa da AMCON din isasshen lokaci, kamata yayi AMCON ta koma bin sulhu wadda ake yi a kotuna kafin a ga alkali, donsamo wasu kudaden, maimakon kai qara kai tsaye.

Shi dai irin wannan sulhu, wanda kamar dai ace sulhu ne ko plea-bargain a turance, ko kuma ace arbitration, wanda za'a iya shiga yarjejeniya da wadanda ake tuhuma, kan yadda zasu biya ko kuma lokutan da zasu biya kudaden bashi ko kadara, ba ma sai an bata lokaci gaban alkali ba.

Wannan uban bashi dai, shima yana haifar da tsaiko, a kokarin farfado da kasar nan daga kangin kaka-nika-yi na tattalin arziki.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel