NiMet: Kano, Yobe da Jihohin Arewa 13 da za a Sheka Ruwan Sama a Ranar Talata

NiMet: Kano, Yobe da Jihohin Arewa 13 da za a Sheka Ruwan Sama a Ranar Talata

  • NiMet ta yi hasashe saukar ruwan sama mai karfi da tsawa a tare da yiwuwar afkuwar ambaliya a yau Talata, 1 ga Yuli, 2025
  • Za a fuskanci tsawa da ruwan sama mai matsakaicin karfi a jihohin Arewa kamar Yobe da Kaduna, tare da yiwuwar ambaliyar ruwa
  • NiMet ta shawarci 'yan Najeriya su yi taka tsantsan yayin da ake ruwa, ta gargadi masu ababen hawa da su kauracewa tuki ana ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da rahoton yanayi na yau Talata, 1 ga Yuli, 2025, inda ta yi hasashen saukar da ruwan sama mai karfi hade da tsawa.

Wannan gargadin na zuwa ne yayin da damina ke ci gaba da kankama kasar, tare da hasashen ambaliyar ruwa za ta iya afkuwa a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

2027: APC ta fadi yadda jihar Sakkwato kadai ta isa kai Tinubu ga nasara a Arewa

Hukumar NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama a jihohin Arewa da Kudu a yau Talata
Ruwan sama zai sauka kamar da bakin kwarya hade da tsawa a jihohin Arewa da Kudu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tsawa da ruwan sama mai karfi a Arewa

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, NiMet ta bayyana cewa yankunan Arewa za su fuskanci washewar sararin samaniya, amma daga bisani hadari zai hadu a safiyar yau Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta yi hasashen cewa za a samu tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a jihohin Yobe, Jigawa, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Gombe, Bauchi da Taraba.

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai karfi tare da tsawa daga yamma zuwa dare a Borno, Jigawa, Yobe, Gombe, Bauchi, Kaduna, Katsina, da Kano.

An shawarci mazauna waɗannan jihohin da su yi taka tsantsan da yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa da kuma gurɓacewar yanayi.

Hasashen ruwan sama a Arewa ta Tsakiya

A yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya, NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci tsawa tare da ruwan sama a safiyar Talata a Plateau, Abuja, Nasarawa, da Neja.

Kara karanta wannan

'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai

Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran ruwan sama mai matsakaicin karfi zai mamaye yankin gaba ɗaya.

An shawarci mazauna waɗannan yankuna da su shirya wa saukar ruwan saman kuma su guji barin abubuwan da iska za ta iya dauka a waje.

Hadari da ruwan sama a jihohin Kudu

NiMet ta bayyana cewa hadari zai hadu a jihohin Kudancin Najeriya tare da yiwuwar saukar ruwan sama a safiyar Talata, musamman a Cross River da Akwa Ibom.

Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran tsawa za ta sauka tare da ruwan sama a jihohin Abia, Imo, Ebonyi, Enugu, Anambra, Edo, Delta, Rivers, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom.

An shawarci mazauna yankin Kudu da su kasance cikin shiri don ruwan saman na iya zuwa da ambaliya, musamman a yankunan da ke gabar teku.

Hukumar NiMet ta gargadi masu ababen hawa da su guji yin tuki yayin da ake ruwan sama
An gargadi masu ababen hawa da su guji yin tuki yayin da ake sheka ruwan sama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Muhimman shawarwari daga NiMet

Hukumar NiMet ta ba da shawarwari masu muhimmanci ga jama'a. Ta ce tsawa na iya zuwa tare da iska mai karfi, don haka ya kamata jama'a su kasance masu lura da kuma daukar matakan kariya.

Kara karanta wannan

Taraba: Mummunan hatsari ya faru a cikin kasuwa bayan motar yashi ta markaɗe mutane

An bukaci masu ababen hawa da su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai karfi don kiyaye afkuwar haɗurra. Kuma a guji neman mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi yayin ruwan sama.

NiMet ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su rika neman rahotannin yanayi daga hukumar yayin da za su shirya tafiye-tafiyen jiragensu.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Ma'aikatan NiMet sun tsunduma yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma’aikatan NiMet sun fara yajin aiki a fadin ƙasar, inda suke zagaye filayen jiragen sama don tabbatar da bin umarnin dakatar da aiki.

A wancan lokacin, sun koka da ƙarancin albashi, suna cewa wasu ma’aikata na karɓar bashi domin biyan haya da kudin makarantar ‘ya’yansu.

Shugaban kungiyar ma’aikata, Paul Ogohi, ya bayyana cewa rayuwar ma’aikatan na cikin haɗari, inda ya ce 70% na fama da hawan jini, 90% kuma na da matsalar ido.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com