'Yan Sanda da 'Yan Bindiga Sun Gwabza Kazamin Fada a Jihohi 3, an Kwato Mutane 29

'Yan Sanda da 'Yan Bindiga Sun Gwabza Kazamin Fada a Jihohi 3, an Kwato Mutane 29

  • 'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane uku kuma sun ceto mutane 29 a ayyukan da suka gudanar a Kogi, Legas da Katsina
  • A jihar Kogi, an ceto mutane 24 bayan musayar wuta da masu garkuwa, tare da kama bindigogi da alburusai a wata mota
  • An kama masu garkuwa uku a Legas bayan sun sace wani matashi ta WhatsApp, yayin da a Katsina 'yan sanda suka ceto mutane huɗu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama mutane uku da ake zargi da garkuwa da mutane a wani samame na musamman kan yaƙi da miyagun laifuffuka.

'Yan sanda sun sami nasarori masu yawa a ayyukan da suka gudanar a jihohin Kogi, Legas, da Katsina, wanda ya kai ga ceton mutane 29 da aka sace.

Kara karanta wannan

'Dan shekara 24 ya yi garkuwa da abokinsa, ya karɓi Naira miliyan 5.3 kuɗin fansa

'Yan sanda sun ceto mutane 29 tare da kama masu garkuwa da mutane 3 a Katsina, Legas da Kogi
Kakakin 'yan sandan Najeriya na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ba da rahoton ceto mutane 29. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

Kakakin hukumar ƴan sanda ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarorin 'yan sanda a Kogi, Legas da Katsina

1. An ceto mutane 24 a Kogi

A ranar 23 ga Yuni, 2025, jami'an 'yan sanda a jihar Kogi sun yi nasarar dakile yunƙurin garkuwa da mutane da ya shafi wasu motocin haya guda uku.

Jami'an da ke sintiri a kan titin Obajana–Oshokoshoko sun yi musayar wuta da masu garkuwar kuma suka yi nasarar ceto mutane 24 da aka sace.

Sanarwar ACP Adejobi ta ce:

"Haka kuma, a ranar 22 ga Yuni, 2025, jami'an 'yan sanda da ke aiki a ofishin Okene, jihar Kogi, sun tare wata mota kirar Nissan a kan hanyar Auchi.
"Direban motar ya tsere zuwa daji, ya bar motar da wata jaka a baya. Binciken da aka gudanar a kan motar, ya kai ga gano bindiga kirar AK-47, harsasai 28 na 5.6mm, gidajen harsasan G3, baƙar riga, da wasu tarkace."

Kara karanta wannan

Taraba: Mummunan hatsari ya faru a cikin kasuwa bayan motar yashi ta markaɗe mutane

2. An kama masu garkuwa 3 a Legas

ACP Adejobi ya ce kwanan nan, jami'an 'yan sanda da ke aiki a jihar Legas, suka karbi rahoton wani lamari na sace mutane a yankin Ikoga na Morogbo.

"An yaudari wani saurayi mai shekaru 20 mai suna Kehinde, ta hanyar WhatsApp kuma wadanda suka yaudare shin suka sace shi, inda suka buƙaci kuɗin fansa na N500,000 daga iyalinsa.
"Aikin 'yan sanda na gaggawa ya kai ga kama waɗanda ake zargi su uku: Celestine Okeke, Michael Okonkwo, da Kehinde Oladun da kuma ceto wanda aka sace."

- ACP Olumuyiwa Adejobi.

Rundunar 'yan sanda ta yi musayar wuta da 'yan bindiga a Katsina, Legas da Kogi
Babban Sufetan 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

3. An ceto mutane 4 a Katsina

A wata nasarar kuma, jami'an rundunar 'yan sanda a Katsina, sun samu rahoton wani hari da yunƙurin sace mutane da aka kai a ƙauyen Mazare na jihar.

Sanarwar ACP Olumuyiwa Adejobi ta ce 'yan sandan sun gaggauta zuwa wurin, suka yi musayar wuta da masu garkuwar.

Kara karanta wannan

Matakan da aka dauka bayan kisan gilla da aka yiwa 'yan Arewa a jihohi 3 na Najeriya

"Jami'an 'yan sanda sun yi galaba a kan masu garkuwar, wanda ya tilasta su tserewa da raunuka daban-daban na harbin bindiga, inda aka ceto mutane hudu da suka sace"

- ACP Olumuyiwa Adejobi.

Karanta sanarwar a kasa:

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar sun dakile hare-haren ‘yan bindiga a wurare biyu yayin wani aiki da suka gudanar.

Rundunar ta shaida cewa ta kuɓutar da mutum 18 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Funtua zuwa birnin Gusau na Zamfara.

Haka kuma, jami’an rundunar 'yan sandan sun hana ‘yan bindiga sace shanu da dama bayan musayar wuta mai zafi tsakaninsu da maharan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com