'An Yi Ƙulle Ƙulle': Jonathan Ya Faɗi abin da Hadimin Yar'Adua Ya Yi Masa da ba Zai Manta ba
- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda aka hana shi karɓar mulki kafin rasuwar marigayi Umaru Musa Yar'Adua
- Jonathan ya ce hadimin shugaban kasar ya ƙi miƙa wasikar da Yar'Adua ya rubutawa majalisar tarayya, lamarin da ya janyo tsaiko mai yawa
- Ya ƙara da cewa an sha ba shi labarin za a yi juyin mulki, har ana tsoratar da shi ya kwana a fadar Aso Villa saboda rikicin siyasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi magana kan kalubalen da ya fuskanta.
Jonathan ya fadi matsalolin da ya ci karo da su musamman lokacin da marigayi Umaru Musa Yar'Adua ya rasu.

Source: Facebook
Yar'Adua: Jonathan ya fadi kalubalen da ya fuskanta
Jonathan ya fadi haka ne yayin hira da yan jaridu a wani faifan bidiyo da TheCable ta wallafa a yau Asabar 28 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, Jonathan ya ce kafin Yar'Adua ya rasu an yi kokarin hana shi rike madafun iko lokacin da jikin marigayin ya yi tsanani.
Ya ce marigayin da kansa ya rubuta wasika zuwa ga majalisar tarayya amma hadimin Yar'Adua ya ki kaiwa wanda ya jawo matsaloli da yawa.
Ya ce:
"Najeriya kasa ce da ta rabu tsakanin Kudanci Kiristoci da Arewa mafi yawa Musulmi, Yar'Adua Musulmi ne daga Arewa wanda ya karba daga dan Kudanci Kirista, Obasanjo wanda ya yi shekaru takwas.
"Tabbas yan Arewa sun so Yar'Adua ya yi shekaru takwas kafin mulki ya koma Kudu amma sai matsalar rashin lafiya ta faru.
"Kun san kafin mataimakin shugaban kasa ya kama aiki sai an tura wasika zuwa ga majalisar tarayya, amma wanda aka ba wasikar da aka rubuta domin ya kai ba zan fadi sunansa ba amma hadimin shugaban kasa ne yaki kai wasikar.
"Jikin Yar'Adua ya kara tsanani ba zai iya yin komai ba a lokacin saboda bai san ma me ake toyawa ba."

Source: Facebook
Yadda aka yada kifar da gwamnatin Jonathan
Jonathan ya ce an bata lokaci sosai babu mukaddashin shugaban kasa wanda hakan ya tilasta majalisa daukar mataki.
Ya ce saboda abubuwan da ke faruwa kullum yana samun labarin cewa za a yi juyin mulki inda har ake tsoratar da shi game da kwana a fadar shugaban kasa.
Amma ya ce duk da haka ya ki bin shawarar wasu da ke ce masa ya sauya wurin kwana zuwa wani wuri saboda fargaba.
Jonathan ya yaba kyawawan halayen Yar'Adua
Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya faɗi kyawawan halayen mai gidansa, tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Ƴar'adua.
Tsohon shugaban wanda ya yi aiki da Ƴar'adua ya bayyana marigayin a matsayin shugaba na gari, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al'umma.
Jonathan ya ce duk da shekara 15 kenan da rasuwarsa, har yanzu ana koyi da kyawawan halayensa na hadin kai, zaman lafiya da, gaskiya da rikon amana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

