Yadda Jonathan ya tuna da Marigayi Yar’adua, shekaru 12 da rasuwarsa a gadon mulki
- Goodluck Ebele Jonathan ya rubuta ta’aziyya na musamman ga Marigayi Umaru Musa Yar’Adua
- A yau Shugaba Umaru Musa Yar’ Adua yake cika shekara 12 da rasuwa yana kan karagar mulki
- A cewar Dr. Goodluck Ebele Jonathan, samun wani tamkar tsohon shugaban Najeriyan zai yi wahala
Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya yabi tsohon mai gidansa, Marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’ Adua.
Jaridar Punch ta rahoto Goodluck Ebele Jonathan yana cewa tsohon shugaban na Najeriya jagora ne mai kishin al’ummarsa, maras son kai.
Shekaru 12 kenan da rasuwar Umaru Musa Yar’ Adua, Dr. Jonathan ya ce samun shugaban kasa irin marigayin yana da matukar wahala.
Jonathan ya fitar da wani sakon ta’aziyya na musamman ne da ya yi wa take da ‘President Yar’Adua: 12 years after’ a shafin Facebook.
Yar’Adua ya rasu ne a rana irin ta yau a shekarar 2010. Marigayin ne ya karbi mulki a hannun Olusegun Obasanjo, amma ya rasu yana ofis.
‘Shugaba Yar’Adua: Bayan shekaru 12."
“Shekaru 12 da suka wuce, kasarmu ta rasa mai kishi, shugaba maras son kai, mai kawo zaman lafiya, wanda yayi mulki da sha’awa da gaskiya.”
“Shugaban kasa Umaru Musa Yar’ Adua ba ya tare da mu a yau, amma tambarin da ya bari a wajen jagorantar al’umma ya sa ana ta tunawa da shi.”
“Kamar ‘dan wasan da yake tsere cikin nishadi, haka ya yi imani har ya kai karshen tseren. A yau za mu iya cewa ya ciri tuta wajen zaman lafiya.”
“Dakare ne na gaskiya, wanda ya yarda da adalci da tsarin damukaradiyya. Jagora na shi mai bautawa al’umma, kuma mutumin kwarai.”
- Goodluck Ebele Jonathan
A karshe Jonathan ya kare sakon ta’aziyyarsa da cewa samun irin Marigayin, yana da wahala.
“Ya kasance mai gidana.”
“Shugaba Yar’adua, a yau mu na tuna ka, kuma za mu cigaba da tuna ayyukan kirkin da ka yi wa kasarmu. Ka nuna kishi da hidimar al’umma.”
- Goodluck Ebele Jonathan
Mutuwar Abiola
Kwanan nan aka ji labari cewa Abdul Abiola ya fito yana kira ga Muhammadu Buhari ya binciki mutuwar mahaifinsu da mai dakinsa, Kudirat Abiola.
Cif MKO Abiola wanda ake tunanin zai lashe zaben 1993, ya mutu ne yayin da yake tsare a kurkuku ana tsakar maganar shirin fito da shi a 1998.
Asali: Legit.ng