"Yadda Aka Wawure N1.09bn daga Asusun Gwamnatin Kogi a cikin Kwanaki 3 kacal"

"Yadda Aka Wawure N1.09bn daga Asusun Gwamnatin Kogi a cikin Kwanaki 3 kacal"

  • Shaidan gwamnati ya bayyana yadda aka cire N1.09bn daga asusun gwamnatin Kogi cikin kwana uku kacal, wanda ya saba dokar CBN
  • Mashelia Arhyel Dada, ma'aikacin Zenith Bank, ya ba da shaida dalla-dalla kan yadda aka riƙa cire kuɗaɗe tsakanin 2016 zuwa 2023
  • Mai Shari'a Emeka Nwite ya ɗage shari'ar zuwa Juma'a, 27 ga Yuni, 2025, domin ci gaba da shari'a da yi wa shaidan karin tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani shaidan EFCC a shari'ar Yahaya Bello, ya bayyana wa kotu yadda aka wawure N1.09bn daga asusun jihar Kogi a cikin kwanaki uku kacal.

Shaidan, mai suna Mashelia Arhyel Dada ya yi bayani ne a gaban Mai Shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja, a ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

PDP ta sake yin babban rashi: Tsohon shugabanta ya riga mu gidan gaskiya

Shaidar EFCC ya fadawa kotu yadda aka karkatar da N1.09bn daga asusun gwamnatin Kogi
EFCC na ci gaba da gabatar da shaidu a shari'ar da ake zargin Yahaya Bello ya sace N80.2bn. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta gabatar da shaida a gaban kotu

Hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook cewa, shaidan ya warware yadda aka rika zare kudade daga asusun gudanarwar gidan gwamnatin jihar Kogi, har suka kai N1,096,830,000 a cikin kwanaki uku kacal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mashelia Arhyel Dada, ya kasance jami'in bin doka ne a bankin Zenith Bank, reshen Maitama, kuma ya ba da shaida a matsayin Shaida na Huɗu (PW4) bisa umarnin kotu.

Ya ba da cikakken bayani kan yawan kuɗin da aka cire daga asusun gidan gwamnatin Kogi a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2023, ta amfani da hanyoyin banki daban-daban.

Yadda aka wawure N1.09bn, aka karya dokokin CBN

Yayin da lauyan gwamnati, Kemi Pinheiro, SAN, ke jagorantar gabatar da shaida, Mashelia Dada ya ce bayanan da ya gabatar suna cikin takardu guda bakwai da aka miƙa biyo bayan umarnin kotu ga shugaban bankin.

An karɓi umarnin kotun a matsayin hujja ta 20, yayin da takardu masu alaƙa da mamallakan asusun bankuna da kamfanoni aka karɓa a matsayin hujjoji na 21 zuwa 24C.

Kara karanta wannan

Jagororin adawa sun dura a kan Trump, an gargade shi kan shiga shari'ar Netanyahu

Daga cikin asusun da aka bincika akwai na Adamu Jagafa Ishaya, Whales Oil and Gas, Jimeda Properties Nigeria Limited, Alyeshua Solutions, da kuma asusun gudanarwa na gidan gwamnatin Kogi.

Da yake mai da hankali kan asusun gidan gwamnatin jihar Kogi, Kemi Pinheiro ya nuna yadda ake yawan cire kuɗi wanda ya taka wasu dokokin CBN na rage amfani da kuɗi masu yawa.

A cewar Mashelia Dada, CBN ya sanya iyakar cire kuɗi a N500,000 ga daidaikun mutane da N5,000,000 ga kamfanoni ko hukumomin gwamnati a lokacin da abin ya faru. Wuce waɗannan iyakoki yana jawo ƙarin cajin baki.

Jerin cire kuɗaɗe daga asusun gwamnatin Kogi

Mashelia Dada ya ba da shaida cewa a tsakanin ranar 30 ga Janairu zuwa 1 ga Fabrairu, 2018, an cire jimillar N697,267,000 a cikin rukunin N10,000,000 ta hanyar cekin banki da aka bayar da sunan wani Abdulsalami Hudu.

Sannan, a ranar 2 ga Fabrairu, 2018, an sake cire ƙarin N99,573,000 a irin wannan tsarin cire kudin da kuma wasu cire-cire da dama waɗanda suka kai N1.09bn cikin kwanaki uku.

Lauyan EFCC ya kuma bayyana cewa a ranar 1 ga Fabrairu, 2018, an fitar da kuɗi N3,325,000 daga asusun gwamnatin Kogi zuwa asusun wani Ali Bello.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ɗage ranar ɗaukar ma'aikata 30,000 a hukumar CDCFIB, ta faɗi dalili

Mashelia Dada ya ƙara bayyana cewa irin waɗannan hada-hadar kuɗi masu ban mamaki sun ci gaba har zuwa wasu shekaru.

A ranakun 6 ga Mayu, 11 ga Mayu, da 19 ga Mayu, 2022, asusun ya karɓi N100m a kowace rana daga asusun kuɗaɗen haraji na jihar Kogi.

Waɗannan shigar kuɗaɗen nan take suka biyo bayan zare kuɗi masu yawa a cikin rukunin N10m, galibi ta hanyar Abdulsalami Hudu da kuma wani mai suna Alhassan Omakoji.

Ana zargin gwamnatin Kogi ta wawure sama da N1bn, kuma ta turawa wasni Abdulsalami Hudu da sauran su
Ana ci gaba da shari'ar Yahaya Bello ta zargin karkatar da sama da N80bn lokacin da yake gwamnan Kogi. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

Ƙarin shaida kan yadda aka wawure miliyoyi

Da yake nuni ga shafi na 395 zuwa 401 na bayanin asusun, shaidan ya tabbatar da cewa kusan duk wani shigar kuɗi nan take yana biyo bayan cirewa ta hanyar cekin banki da aka bayar ga waɗannan mutanen, wani lokacin ma a rana ɗaya.

Mashelia Dada ya kuma bayyana cewa a ranar 7 ga Satumba, 2023, an cire kuɗi kai tsaye daga asusun har sau 11, kuama ana cire N10m ne, wanda ya haura iyakar N5m.

Ya ce saboda kudin sun haura ka'idar CBN, sai da aka rika cajar N500,000 kan kowace hada-hada. Wannan ya haifar da jimillar cajin kudi na N4,750,000 a ranar kaɗai.

Kara karanta wannan

An kashe yaran Sheikh Ibrahim Khalil a Benue, gwamnan Kano ya yi magana mai zafi

A wani misali kuma, a ranar 20 ga Janairu, 2018, asusun ya karɓi shigar kuɗi daban-daban har sau 10 daga asusun kuɗaɗen haraji na jihar Kogi waɗanda suka kai sama da N697m.

Waɗannan sun sake biyo bayan jerin cire-ciren N10m da aka ba Hudu da sauran su. A ranar 31 ga Janairu, an ruwaito Hudu kaɗai ya karɓi N347,267,000 a cire kuɗin da aka yi sau 36.

An ɗage shari'ar zuwa ranar Juma'a, 27 ga Yuni, 2025, don yi wa shaidan tambayoyi da kuma ci gaba da shari'ar.

Yahaya Bello ya roki alfarmar EFCC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, yayin da shari’ar zargin badakalar N80.1bn ke ci gaba da gudana, Yahaya Bello ya roki EFCC da ta sauya wurin tuhumarsa daga Abuja zuwa Kogi.

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa bai kamata a ci gaba da gurfanar da shi a Abuja ba, kasancewar laifin da ake zarginsa da aikatawa bai faru a nan ba.

Saboda haka, ya bukaci hukumar EFCC da ta dawo da shi jihar Kogi domin ci gaba da shari’ar, maimakon a ci gaba da tsare shi a babban birnin tarayya, Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com