CBN Ya Kara Adadin Kudaden Da ’Yan Najeriya Za Su Iya Cire Duk Sati Zuwa N500k

CBN Ya Kara Adadin Kudaden Da ’Yan Najeriya Za Su Iya Cire Duk Sati Zuwa N500k

  • Babban Banki Najeriya (CBN) ya yi ingantayya ga dokokin da ya kawo na kayyade adadin kudaden da 'yan Najeriya za su iya cirewa
  • A baya bankin ya ce, mutum ba zai iya cire sama da N100,000 ba, kamfani kuma karkari ya cire N500,000
  • A sabuwar dokar da ta fito daga bakin a cikin wata sanarwa, an ce mutum zai iya cire N500,000, kamfani kuma N5m

Wata sanarwar da Legeit.ng Hausa ta samo daga Babban Bankin Najeriya (CBN) ta gayyana cewa, bankin ya kara adadin tsabar kudi da 'yan Najeriya za su iya cirewa a asusun banki duk mako zuwa N500,000, yayin da kamfanoni za su iya cire Naira miliyan 5 duk mako.

Wannan karin na zuwa ne a cikin wata wasika da CBN ya aikewa dukkan bankunan kasar nan a ranar Laraba 21 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

An Kuma, Kotu Ta Sake Daure Mama Boko Haram Da Wasu Mutum 2 Kan Damfarar N120m

Babban bankin ya yanke wannan shawarin ne bayan sauraran korafe-korafe daga daga masu ruwa da tsaki a Najeriya.

An sake inganta dokar kayyade kudaden da 'yan Najeriya za su iya cirewa a banki
CBN Ya Kara Adadin Kudaden Da ’Yan Najeriya Za Su Iya Cire Duk Sati Zuwa N500k | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ga mutanen da suke sha'awar cire sama da N500,000, CBN ya basu damar hakan, amma za su biya kasho 3% na kudin da suke son cirewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika ga kamfanonin da ke son cire sama da N5m, za su biya kashi 5% na adadin kudin da suke son cirewa, kamar yadda yazo a sanarwar da muka samo.

A bangare guda, bankuna ba za su ke biyan cekin da aka ba wani ba da ya haura N100,000, sabanin yadda dokar baya ta kayyade da N50,000.

Mun ji dadin kara adadin kudin da za a cire

Wani mai sana'ar hada-hadar kudi na POS, Nasiru Ibrahim Yusuf ya bayyana martaninsa bayan kara adadin kudin da mutum zai cire a banki.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya Ya Jero Wadanda Za Su Fi Shan Wahalar Canjin Kudi da Aka Yi

A cewarsa:

"Zan iya cewa na ji dadin karin, saboda a sana'ata nan, ina iya yin cinikin Naira miliyan 2 a rana, to ka ga asusun da nake dashi na kasuwanci idan zan cire Naira miliyan 5 zan yi maleji a satin, kuma mutane suna kara wayewa da tura kudi ta USSD da manhajar waya.
"Kalubalen dai har yanzu daya ne, tunda ana so wannan lamarin ya yi aiki, ya kamata a inganta sabis na kamfanonin layuka da bankuna saboda yawanci tsoron sabis ke sa mutane ke suna karbar 'cash' [tsabar kudi]."

Yadda dokar ta faro

Idan baku manta ba, a farkon makon watan Disamba ne CBN ya bayyana cewa, ya kayyade kudaden da 'yan Najeriya za su iya cirewa a bankunan kasar nan zuwa N100,000, yayin da kamfanoni za su iya cire N500,000.

Wannan doka na zuwa ne jim kadan bayan da babban bankin ya sauya fasalin kudin kasar tare da bayyana sabbin dokokin mu'amalantar kudinta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Ya Yi Babban Rashi, Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP Ya Rasu

'Yan Najeriya da dama sun bayyana bacin ransu tare da yin martani mai zafi game da sabbin ka'idojin da bankin ya sanyawa 'yan Najeriya.

Wannan sauyi ko gyara doka zai amsa kadan daga tambayoyin da 'yan Najeriya ke yi na meye dalilin kakaba musu ka'ida kan kudadensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel