'Yan Bindiga Sun Nuna Tsaurin Ido, Sun Kashe Sojojin Najeriya 20 a Neja

'Yan Bindiga Sun Nuna Tsaurin Ido, Sun Kashe Sojojin Najeriya 20 a Neja

  • Akalla sojoji 20 ne suka mutu a harin da ‘yan bindiga suka kai sansanin soji da ke Kwanan Dutse, ƙaramar hukumar Mariga, jihar Neja
  • Yayin da aka kai gawarwakin zuwa asibiti, wata majiya ta ce akwai sojoji da dama da suka jikkata a harin ƴan bindigar na safiyar Talata
  • Harin ya zo bayan kashe mutane 15 a Zamfara da kuma artabun sojoji da Bello Turji a Sokoto wanda ya yi ajalin mutane 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Wasu hatsabiban ƴan bindiga sun tafka ɓarna a wani mummunan hari da suka kai sansanin sojojin Najeriya a jihar Neja.

Akalla sojoji 20 ne suka rasa rayukansu a wannan harin, bayan ‘yan bindigar sun buɗe masu wuta a sansaninsu da ke Kwanan Dutse, karamar hukumar Mariga.

'Yan ta'adda sun farmaki sansanin sojojin Najeriya da ke Neja, sun kashi jami'ai 20
Dakarun sojin Najeriya yayin da suke aikin kakkabe 'yan ta'adda a cikin dazuka. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Ƴan bindiga sun kashe sojoji 20 a Neja

Kara karanta wannan

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Neja da Kaduna, an yi asarar rayuka

Wata majiya daga sashen tsaro a karamar hukumar Shiroro, ya shaidawa Premium Times yadda harin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda rashin izinin magana da manema labarai ta ce an kai harin ne a safiyar ranar Talata.

Baya ga sojoji 20 da aka kashe yayin harin, majiyar ta ce ƴan ta'addar sun kuma raunata wasu sojojin da dama.

Ta kuma ƙara da cewa an kai gawarwakin sojojin da suka mutu asibiti, amma ba ta bayyana asibitin da aka kai su ba.

Babu martani daga hukumomin tsaro kan harin

Rundunar soji ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba tukuna, kalmar yadda jaridar ta wallafa.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, mai magana da yawun rundunar soji, Onyechi Anele, bai amsa sakonnin da aka aika masa ba.

Shi ma kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Neja, Abdullahi Garba, bai mayar da martani ba game da harin, a cewar rahoton Sahara Reporters.

Harin ya auku ne sa'o’i kaɗan bayan da ‘yan bindiga suka kashe mutane kusan 15 a kauyen Tofa da ke gundumar Magami, karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Ana cikin murnar tsagaita wuta, bam ya tarwatse da sojojin Isra'ila a Zirin Gaza

'Yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a harin da suka sansanin soji a Neja
Sojojin Najeriya suna rangadi a dazukan Najeriya domin kakkabe 'yan ta'adda. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Hare-haren da aka yi kafin harin Neja

A wannan ranar ne kuma aka yi wani kazamin artabu tsakanin sojoji da ayarin fitaccen ɗan bindiga Bello Turji a jihar Sokoto.

Wannan artabu ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100 a kusa da kauyen Cida da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Sokoto.

A dangane da harin jihar Neja kuwa, har zuwa yanzu ba a samu wata kungiyar ‘yan bindiga da suka ɗauki alhakin harin da aka kai wa sojojin ba.

Amma wata majiya ta shaida cewa yankin da aka kai harin na daga cikin yankunan da dabar Dogo Gide da ragowar ƴan dabar marigayi Ali Kawaje ke da iko da su.

'Yan bindiga sun farmaki kauyuka a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hankula sun tashi a jihar Neja bayan wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai wa al'ummomi.

An kiyasta cewa adadin 'yan bindigar sun haura mutum 100, kuma sun afka wa kauyuka uku a wata karamar hukuma.

Miyagun 'yan bindigar sun bi kauye-kauye, suna aikata ta'addanci ba tare da wani shamaki ba. Wannan lamarin ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com