Haraji: Nyesom Wike Ya Fadi Manyan Abuja da ke Jawo Masa Matsala
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa babban cikas wajen tattara haraji shi ne rashin biyan haraji daga manyan mutane
- Wike ya jaddada cewa babu wata hanya da gwamnati ke samun kuɗi a Abuja sai kuma ta kudin haraji da sauran mazauna birnin ke biya
- Ministan ya yi barazana ga mazauna Abuja da ke kin biyan kudin haraji, inda ya ce za a iya wallafa sunayensu a jaridun kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana babban abin da jawo cikas wajen tattara haraji a yankin.
Ministan ya ɗora dukkanin kalubalen tattara haraji da ake fuskanta a kan 'manyan mutanen da suke hana ruwa gudu a Abuja.

Kara karanta wannan
Sanata Ningi ya dauki zafi, yana son majalisa ta binciki rashin biyan yan kwangila hakkokinsu

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Wike ya fadi haka ne a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da sabon titin CN2 daga Ahmadu Bello Way a Mabushi zuwa unguwar Katampe da shugaba Bola Tinubu ya kaddamar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyesom Wike ya fusata da 'manyan' Abuja
Business Day ta ruwaito Ministan ya ce abin takaici ne yadda wasu daga cikin waɗanda ke ƙin biyan haraji a Abuja wanda ke taimaka wa wajen kara matsalolin da ake fama da su.
Ya ce:
“Ga waɗanda muke rufe gidajensu saboda ƙin biyan haraji, ku duba, ku gani da idonku: wannan shi ne abin da ake iya yi idan an biya hakkokin gwamnati. Idan ba ku biya ba, wa zai kawo wannan ci gaba?”

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar mutane su canza ra’ayi domin ci gaban birnin, inda ya jaddada cewa Abuja ba ta da wata hanya ta samun kuɗi illa haraji da sauran kuɗin da mazauna ke biya.
Wike ya kara da cewa:
"Idan ba ku biya ba, babu wanda zai samar da wannan ababen more rayuwa domin abu ɗaya tilo da birnin ke da shi shi ne tara haraji. Mutane suna cewa Abuja ta wadata. Ta wadata da me?"
Nyesom Wike ya roki Bola Tinubu
Ya roƙi Shugaba Bola Tinubu, wanda Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya wakilta, da ya yi magana da mazauna Abuja kan muhimmancin biyan haraji.
Ya ce yin hakan zai bai wa Hukumar babban birnin damar samar da ƙarin ababen more rayuwa a yankin don amfanin kowa da kowa.
Ya tunatar da mazauna Abuja, musamman masu kuɗi, cewa duk wanda ke da fili a yankin kuma bai biya haraji ba, ya kamata ya biya.
Nyesom Wike ya yi barazanar cewa in ba haka ba za a wallafa sunayensu a jaridu a matsayin masu kin biyan hakkokinsu.
Ya jaddada cewa ba talaka ke da ƙarfin gina gida a Katampe da Mabushi ba, yana ƙara da cewa masu gina gidaje a waɗannan yankuna manyan 'yan kuɗi ne.
Wike ya kai tsofaffin gwamnoni ga Tinubu
A baya, mun wallafa cewa Nyesom Wike, ya kai wasu tsofaffin gwamnonin jam’iyyar PDP guda uku sun gana da shugaban ƙasa, Bola Tinubu a fadar gwamnati da ke Aso Rock, Abuja.
Wike ya jagoranci tsofaffin gwamnonin PDP da suka hada da Ayodele Fayose na jihar Ekiti, Samuel Ortom na jihar Binuwai, da Okezie Ikpeazu na jihar Abia ga fadar shugaban kasa.
Dukannin tsofaffin gwamnonin sun kasance daga cikin ƙungiyar G5 — wata ƙungiya da ta fito fili wajen kalubalantar shugabancin jam’iyyar PDP a lokacin shirin zaɓen 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

