Kazamin Fada Ya Barke tsakanin Jami'an Tsaro da Bello Turji, an Samu Asarar Rayuka 100
- Mummunan faɗa ya ɓarke tsakanin jami'an tsaro na rundunar Askarawan Zamfara da mayaƙan tantirin ɗan bindiga, Bello Turji
- Fadan ya yi sanadiyyar rasa rayukan mayaƙan Bello Turji masu yawa da wasu daga cikin jami'an tsaro
- An kai farmakin ne don cafke Bello Turji a mace ko a raye, amma sai ya shiryawa jami'an tsaro kwanton ɓauna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - An samu asarar rayuka bayan faɗa ya ɓarke tsakanin mayaƙan Bello Turji da jami'an rundunar Askawaran Zamfara.
Fiye da mutane 100 aka ruwaito an kashe a artabun wanda ya auku a kusa da ƙauyen Ruggar Chidda da ke cikin ƙaramar hukumar Shinkafi.

Source: Twitter
Wani mazaunin yankin, Sa’idu Garba, ya shaidawa The Punch cewa Askarawan Zamfara tare da taimakon CJTF, sun kai hari kan sansanin Bello Turji da nufin cafke shi a raye ko a mace.

Kara karanta wannan
Matashi ya hau kan dogon ƙarfe a Kano, ya buƙaci wasu fitattun mutane su je wurin
Jami'an tsaro sun fafata da mayaƙan Bello Turji
An ce wani tsohon ɗan bindiga da ya tuba, Bashari Meniyo, ne ya jagoranci wannan farmakin.
"Sun tattaru ƙarƙashin jagorancin wani tsohon ɗan bindiga da ya tuba mai suna Bashari Meniyo, suka nufi sansanin Bello Turji da niyyar kama shi, a raye ko a mace, ba tare da sanin jami’an tsaro ba."
"Amma abin da ba su sani ba shi ne, Turji ya samu labarin cewa suna shirin kai masa hari, don haka ya hanzarta ya tara mayakansa, waɗanda suka haura 1,000."
"Faɗa mai tsanani ya gudana tsakanin ɓangarorin biyu har na tsawon awanni ba tare da shiga tsakani daga jami’an tsaro ba."
“Ko da yake Bello Turji ya tsira da ƙyar, an kashe sama da mutum 100 daga cikin mutanensa a yayin faɗan."
- Sa'idu Garba
Bello Turji ya kashe jami'an tsaro
Ya kuma tabbatar da cewa mayaƙan Bello Turji sun kashe fiye da mambobi 20 na Askarawan Zamfara, ciki har da Bashari Meniyo.
"Bashari Meniyo, wanda ya jagoranci mambobin Askawaran Zamfara, ya mutu tare da wasu daga cikin tawagarsa."
"Idan da jami’an tsaro sun isa yankin lokacin da faɗan ke gudana, da an kashe Bello Turji."
- Sa'idu Garba
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa aƙalla mambobi 40 na Askawaran Zamfara da CJTF aka kashe a kwanton ɓaunan da Bello Turji ya yi musu.

Source: Original
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar sojoji, Laftanar Kanal Suleiman Omale, bai yi nasara ba domin wayarsa a kashe take, sannan bai mayar da amsar saƙonnin da aka tura masa ba.
Da aka tuntuɓi mataimaki na musamman ga Gwamna Dauda Lawal kan Harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Mustafa Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba zai iya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.
"Dole ne sai na binciko adadin mambobin Askarawan Zamfara da CJTF da ake cewa sun mutu kafin na fitar da wata sanarwa. A yanzu haka ba zan iya cewa komai ba sai bayan an kammala bincike."
- Mustafa Kaura
Bello Turji ya ƙaƙabawa manoma haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa hatsabibin ɗan bindiga Bello Turji ya ƙaƙaba haraji kan manoman da suke son yin noma.
Tantirin ɗan bindigan ya buƙaci manoma a Zamfara da su biya shi miliyoyin kuɗi domin ya bari su yi noma.
Turji ya bukaci N50m daga mazauna Tsallaken Gulbi a ƙauyen Fakai da ke ƙaramar hukumar Shinkafi a Zamfara a matsayin kuɗin haraji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

