"Mutane Su Daina Tsoro," Ƴan Sanda Sun Gano Abin da Ya Fashe Ya Kashe Mutum 5 a Kano
- Rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton da ke yawo cewa bam ne aka dasa kuma ya fashe tare da kashe mutane biyar a Kano
- A wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ta fitar, ta ce wani abun fashewa na UXO da aka haɗo da kayan yan gwangwan ne ya tarwatse, ba bam ba
- Rundunar ta buƙaci mutanen Kano su kwantar da hankulansu, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta ce fashewar da ta faru a titin Eastern Bypass ta jihar ba bam (IED) ba ne kamar yadda ake zargi tun da farko.
Rundunar ta bayyana cewa wani abin fashewa na sojoji (UXO) ne ya tarwatse ba bam ba kamar yadda mutane ke ta yaɗawa.

Source: Original
Mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, Hussaini Abdullahi, ne ya bayyana hakan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Yan sanda sun gano abin da ya fashe a Kano
Ya ce binciken da tawagar sashen kwance bam da sauran ababen fashewa ta gudanar, ya nuna cewa sindarin fashewa na UXO ne ya fashe ba bam da ake ƙerawa (IED) ba.
Hussaini Abdullahi ya ce san sako kayan fashewar ne a cikin kayan ƴan gwangwan daga Jihar Yobe, ba tare da an sani ba, kuma daya daga cikinsu ne ya tarwatse a Kano.
Ya ƙara da cewa, ƴan sanda sun gano jimillar kayan fashewa na UXO guda tara (9) daga wajen da lamarin ya faru, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama, a cewar rahoton Daily Trust.
Abin da aka gano bayan tashin bam a Kano
A cewarsa:
“Biyo bayan fashewar da ta faru a kamfanin ƴan gwangwan Yongxing Steel da ke kan titin Ring Road, unguwar Mariri, Kano, da misalin karfe 11:30 na safe ranar Asabar, 21 ga Yuni, 2025, an gudanar da bincike kan lamarin.
"Binciken bayan da dakarun EOD-CBRN suka gudanar ya nuna cewa s fashewa ne da ba su fashe ba (UXO) suka haddasa lamarin, ba bam da aka kirkira ba (IED) kamar yadda aka yi zargi tun farko.
“An kawo kayan fashewar ne ba da gangan ba a cikin tarkacen karafa daga Jihar Yobe, kuma daya daga cikinsu ne ya fashe a lokacin da ake sauke kayan a nan Kano."

Source: Facebook
Yan sanda sun kwantar da hankulan jama'a
A bisa haka, rundunar tana kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da gujewa firgici, domin babu wani barazanar tsaro da ke tunkaro su.
“Baya ga UXO guda 7 da muka gano daga cikin kayan a farko, an sake gano guda 2 daga wajen da lamarin ya faru, wanda hakan ya kawo adadin zuwa guda 9.”
“Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a fashewar, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa," in ji shi.
Almajirai sun sha guba a shayi a Kano
A wani labarin, kun ji cewa almajairai biyu sun rasu sakamakon shan wani abu da zargin guba ce a jihar Kano.
Lamarin wanda ya afku ranar Juma'a bayan almajiran sun sha wani abin da suka dauka madarar gari ce, da wani ya jefo cikin gidansu ta katanga.
Mazauna yankin sun bayyana kaɗuwarsu da faruwar lamarin amma sun tabbatar da cewa za a gudanar da binciken gawa kafin birne almajiran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


