Mota Dauke da Bam Ta Tarwatse a Kano, Mutum 5 Sun Kwanta Dama

Mota Dauke da Bam Ta Tarwatse a Kano, Mutum 5 Sun Kwanta Dama

  • Rahotanni sun ce wata mota mai ɗauke da kayan fashewa daga Jihar Yobe ta tarwatse a Kano tare da jikkata bayin Allah
  • Kwamishinan yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori da ya tabbatar da al'amarin ya ce an kwashi mutane 15 zuwa asibiti
  • CP Bakori ya ce duk da babu tabbacin musabbabin tarwatsewar motar, amma ana kyautata zaton bam ne samfurin sojojin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Akalla mutane biyar ne suka mutu, bayan da wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar 'bam' da ake zargin samfurin na sojoji ne a birnin Kano.

Lamarin ya afku a safiyar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025 a hanyar Eastern by pass, a daidai wani kamfanin yan gwangwan da ke yankin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe mutane 15 a ranar da Tinubu ya je Kaduna

Ana tsoron bam ya tashi a Kano
Mota dauke da bam daga Yobe ta fashe a Kano Hoto: Salik Ibrahim
Source: UGC

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin, tare da jawo hankalin jami’an tsaro da na agajin gaggawa da su ka kai dauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Bam' ya fashe a jihar Kano

Daily Post ta wallafa cewa Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya isa wurin da lamarin ya faru ba da jimawa ba.

Ya ce fashewar na iya kasancewa ta fito daga wani bam mai karfin gaske da ake kyautata zaton na soji ne da aka dauka ko aka sarrafa shi ba yadda ya dace ba.

Kwamishinan ya kara da cewa:

“Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai muni ya faru. Da na isa wurin, sai na gano cewa wani abu da ake zargin bam ne ya fashe – watakila bam ne na soji. Mutane 15 sun jikkata, sannan biyar sun mutu."

Ya kara da cewa an gaggauta kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibitoci da ke kusa da wurin.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun shammaci mutane da dare, sun dauke liman da mutum 5

'Yan sandan Kano na binciken fashewar bam

Rundunar yan sandan Kano ta tabbatar da cewa ana zurfafa bincike domin gano ainihin abin da ya fashe da dalilin hakan da safiyar Asabar.

Mutane 5 sun rasu a tashin bam a Kano
Mutum 15 bam din ya jikkata bayan ya tashi a Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“Har yanzu ana gudanar da bincike, amma mun samu rahoton cewa motar da ke dauke da kayan fashewar ta fito daga Jihar Yobe.
“Rahotannin farko sun nuna cewa kayan fashewar na cikin wata babbar mota ce, amma har yanzu ba a tabbatar ko ta sojoji ce ko kuma na wasu ba."

Kwamishinan ya ce hukumomi har yanzu ba su kammala bincike ba dangane da musabbabin fashewar da kuma asalin kayan fashewar.

Bam ya fashe a birnin tarayya Abuja

A wani labarin, kun ji cewa wani abu da ake zaton bam ne ya tashi a wata tashar motoci da ke kusa da barikin sojojin Najeriya na Mogadishu da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, 26 ga watan Mayu, 2025, inda ta shaida cewa lamarin ya jefa jama'a cikin fargabar abin da je ya zo.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, ana zargin wani mutum ne ya yi yunkurin kai harin kunar bakin wake, amma ya rasa ransa a lokacin da bam ɗin ya fashe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng