'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Wani Mummunan Hari a Kebbi
- An shiga jimami a jihar Kebbi biyo bayan wani mummunan harin ta'addancin da ƴan bindiga suka kai kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
- Ƴan bindigan sun hallaka mutane da dama a yayin harin wanda suka kai a ƙauyen Tadurga da ke ƙaramar hukumar Zuru
- Tantiran sun kuma yi awon gaba da wasu mutane zuwa cikin daji, tare da sace shanu a harin wanda suka kai cikin dare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Wasu miyagu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a garin Tadurga da ke ƙaramar hukumar Zuru ta jihar Kebbi.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Litinin, inda suka kashe mutane da dama waɗanda ba a tabbatar da adadinsu ba, yayin da suka yi garkuwa da wasu kuma suka sace dabbobi.

Source: Facebook
Wani mazaunin garin mai suna Audu Sule ya ya tabbatar da aukuwar lamarin ga tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Kebbi
Audu Sule ya bayyana cewa maharan sun zo garin da yawansu, inda suka riƙa harbi ba kakkautawa tare da haddasa firgici a tsakanin jama’a.
"Sun shigo da yawa, suna harbi a ko’ina, suka ɓalle shaguna suna sace kaya, sannan suka kashe mutane da dama, suka yi garkuwa da wasu, sannan suka sace shanunmu."
- Audu Sule
Wannan hari na baya-bayan nan na iya yin tasiri wajen rusa ci gaban da aka samu a yaki da ƴan bindiga tun bayan da Gwamna Nasir Idris ya hau mulki.
Wani mazaunin yankin, Abdullahi Zuru, ya ce ƙoƙarin da gwamnatin ke ci gaba da yi ya taimaka wajen korar ƴan bindiga daga yankin, lamarin da ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu har ma suka samu amfanin gona mai yawa.
"Duk da wannan harin da aka kai kwanan nan, masarautar Zuru na samun zaman lafiya."
- Abdullahi Zuru

Source: Original
Me ƴan sanda suka ce kan harin?
Legit Hausa ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Nafiu Abubakar ya bayyana cewa zai bincika domin samun cikakkun bayanai kan harin.
"Eh bari na bincika domin samun ƙarin bayani."
- Nafiu Abubakar
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a sake ji daga gare shi ba.
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- Shirin da gwamnatin Katsina ke yi wa tubabbun 'yan bindiga
- Gwamna ya fusata bayan 'yan bindiga sun hallaka kusan mutum 200, ya sha alwashi
- 'Yan bindiga sun farmaki fadar basarake a Kaduna, an tafka barna
Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tantiran ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun hallaka jami'an tsaron ne a wani hari da suka kai a ƙauyen Marmara da ke cikin ƙaramar hukumar Malumfashi.
Maharan sun kuma yi ajalin tulin manoma waɗanda ba a riga aka bayyana adadinsu ba, a harin da suka kai a ƙauyen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


