Benue: Yan Bindiga Sun Banka wa Gidaje da Ƴan Gudun Hijira Wuta, Mutane Fiye da 200 Sun Mutu
- Ana fargabar kimanin mutane 200 sun rasa rayukansu da wasu miyagun makiyaya suka kai farmaki kauyuka biyu a yankin Guma a jihar Benuwai
- Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda ake fargabar sun mutu a mummunan harin har da yan gudun hijira da jami'an tsaro
- Babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ko gwamnatin Benuwai kan lamarin amma an ce ana ci gaba da tantance ɓarnar da maharan suka yi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Kimanin mutane 200, ciki har da 'yan gudun hijira (IDPs) da jami'an tsaro ake fargabar sun mutu a wasu munanan hare-hare da aka kai a jihar Benue.
Maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne ɗauke da bindigogi sun kashe mutanen a garuruwan Yelewata da Daudu da ke ƙaramar hukumar Guma a Benuwai.

Source: Original
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya auku ne a daren jiya Juma'a, 13 ga watan Yuni, 2025.
Yan bindiga sun tafka ɓarna a Benuwai
Har ila yau, an ce mutane da dama sun jikkata a harin wanda ya zo kwana kadan bayan jama’ar yankin sun samu saƙon barazanar kawo masu hari daga ƴan ta'adda.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga garin Yelewata daga bangarori biyu, suka fatattaki matasa da ƴan sandan da suka tare su da nufin kare al'umma.
Daga nan ne kuma maharan suka bude wuta kan mutanen gari da ‘yan gudun hijira da ke boye a cikin rumfunan kasuwa.
Wani ganau ya ce an kashe mutane da yawa, sannan maharan suka banka masu wuta suka ƙone ƙurmus a gidaje da rumfunan kasuwa, kuma yawancin wadanda suka rasa rayukansu yara ne da jarirai.
Matasa da jami'an tsaro sun tari maharan
Ana cikin haka ne, wata tawagar ta daban ta maharan suka kai hari a garin Daudu, sai dai sun fuskanci turjiya daga matasa da jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin jami’an tsaro.

Kara karanta wannan
Benue: 'Yan bindiga sun shiga gida gida da tsakar dare, sun yi wa bayin Allah kisan gilla
Wani jagoran al’umma a Yelewata kuma tsohon shugaban Hukumar SUBEB ta Benue, Matthew Mnyan, ya ce wannan rana ce ta bakin ciki ga al’ummar Yelewata, Daudu, Guma da jihar gaba ɗaya.
A rahoton Daily Trust, Matthew Mnyan ya ce:
“Harin ya fara da misalin karfe 11 na dare lokacin da ‘yan ta’addan Fulani suka shigo daga yammacin Yelewata suka fara harbi.
"Sai matasa da ‘yan sanda suka yi kokarin dakatar da su. Amma wata tawagar daban ta shigo daga gabashin kauyen, suka fi karfin masu kare kauyen.
“Sun kashe mutanenmu, suka zuba fetur a rumfunan kasuwa suka kona su. A cikin rumfunan, akwai mutane daga Branch Udei da sauran kauyuka da suka dawo nan saboda akwai ‘yan sanda da sojoji kusa.
Ana zargin sama da mutum 200 sun mutu
Mnyan ya ƙara da cewa sun tattara bayanan mutane fiye da 200 da ke zaune a rumfunan da ake kyautata zaton maharan sun ƙona su har lahira.
"Wasu iyalai ne na mutum 15, wasu iyalai 12, maza da matansu da yaransu gaba ɗaya an kona su. Abin tausayi ne matuka," in ji shi.

Kara karanta wannan
Hormuz: Bayan ruwan wuta a Isra'ila, Iran ta toshe hanyar kai mai kasashen duniya
Mai ba Gwamnan Benuwai shawara kan harkokin tsaron cikin gida, Cif Joseph Har, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:
“Ba zan iya bayar da cikakken bayani ba tunda ban halarci wurin da kaina ba, amma na san wannan lamari ya faru a jiya a Yelewata da Daudu. Hari biyu ne daban-daban.”

Source: Twitter
Sojoji da ƴan sanda nawa aka kashe a harin?
Wata majiya daga rundunar soji, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce sojoji biyu sun rasa rayukansu a harin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai ta bakin mai magana da yawunta, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta fadi yawan wadanda suka mutu ba.
Yan bindiga sun kashe mutane 26 a Benuwai
A wani labarin, kun ji cewa mutane 26 sun rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare da ƴan ta'adda suka kai cikin dare a jihar Benuwai.
Rahotanni sun ce ƴan ta'addan sun yi wa mutane 25 kisan gilla a Mtswenem da Akondotyough Bawa da ke yankin North Bank a Makurdi.
Haka nan kuma, mutum ɗaya ya rasa ransa a wani harin daban da aka kai Kenvanger da Agbami a gundumar Mbatyula ta karamar hukumar Katsina-Ala.
Asali: Legit.ng
