Kwacen Waya: Ƴan Sanda Sun Hana Zirga Zirgar Babura, Yawo da Makami a Gombe
- Rundunar 'yan sandan Gombe ta haramta daukar muggan makamai yayin bukukuwa da taruka don dakile ayyukan 'yan daba da ta da hankali
- An hana amfani da babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe, da daukar fiye da mutum daya da amfani da kararrawar manyan mota a babur
- Kwamishinan 'yan sanda, CP Bello Yahaya ya bukaci shugabanni da iyaye su fadakar da jama'a, yana mai cewa za a gurfanar da masu karya doka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Rundunar 'yan sanda a jihar Gombe ta dauki tsauraran matakai bayan kashe-kashe da ake yi a jihar.
Rundunar yan sanda ta sanar da haramta daukar mugaye makamai a fili yayin bukukuwa da taruka don kare lafiyar jama'a.

Source: Facebook
Kakakin jami'an yan sanda a Gombe, Buharee Abdullahi Dam Roni shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka hallaka matashi a Gombe
Wannan matakin yana daga cikin dabarun dakile tada zaune tsaye da ayyukan Kalare, musamman yayin bukukuwa da gangamin jama'a a fadin jihar.
Hakan ya biyo bayan kisan wani matashi da ake zargin yan kalare sun yi a daren ranar Lahadi 8 ga watan Yunin 2025.
An tabbatar da cewa marigayin mai suna Ahmed Kasiran ya rasa ransa ne a unguwar Hammadu Kafi da ke yankin Akko a Gombe.
Majiyoyi sun tabbatar da a lokacin bukukuwan sallah wasu matasa da ke guje-guje a kan babura sun banke wani har lahira bai ji ba bai gani ba.
Lokutan da aka haramta hawa babura a Gombe
Kwamishinan 'yan sanda CP Bello Yahaya ya bayyana cewa kundin tsarin mulki da dokokin laifi sun haramta rike makamai ba bisa ka’ida ba.
Haka kuma, rundunar ta haramta amfani da babura daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe domin hana aikata laifuka da matsaloli.

Kara karanta wannan
Wutar lantarki ta yi ɓarna, babban jami'i a gwamnatin Gombe da wasu mutum 4 sun rasu
An kuma hana daukar fiye da mutum daya a babur da amfani da kararrawar manyan mota da ke haddasa hayaniya daga babura.

Source: UGC
Rokon yan sanda ga shugabanni da sarakunan Gombe
Jami’an tsaro za su tabbatar da bin wadannan dokoki, kuma duk wanda aka kama da karya su zai fuskanci hukunci a kotu.
Rundunar ta bukaci sarakuna, shugabannin al'umma, iyaye da kungiyar masu babura su fadakar da jama'a kan sababbin dokokin.
An kuma bukaci jama'a su rika kai rahoton duk wanda ya karya dokokin ga ofishin 'yan sanda mafi kusa ko ta layukan gaggawa.
Wakilin Legit Hausa ya tattauna da wasu a Gombe
Yayin da wakilinmu ya zagaya birnin Gombe washegari da sanya dokar, mazauna birnin sun koka kan dokar.
Alhaji Yahaya Abubakar ya ce ina ma a ce karfe 9:00 dokar za ta fara aiki da zai fi.
Ya ce:
"Gaskiya lokacin da aka sanya dokar ya yi kusa saboda karfe 7:00 ko sallar Isha ba a yi ba."
Wani dan acaba mai suna Bashir Yahaya ya ce:
"A gaskiya an dakile su kuma hakan zai kawo matsala gare su da kuma tattalin arziki."
Yan kalare sun farmaki DPO a Gombe
Kun ji cewa rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ƙungiyar yan Kalare a Gombe, inda aka kai wa babban dan sanda, CSP Adamu Alhaji-Idi farmaki.
Majiyoyi sun ce lamarin ya afku ne ana tsaka da taron sulhu tsakanin kungiyoyin yan daban, sai suka hade kai tare da kai wa DPO hari.
Rundunar ‘yan sanda ta Gombe ta tabbatar da cafke mutane 25 da ake zargi da hannu a harin, kuma ana ci gaba da bincike don zakulo wadanda ake zargi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

