Za a Yi Zanga Zanga a Jihohi 20 yayin da Tinubu zai Yi Murnar Ranar Dimokuradiyya

Za a Yi Zanga Zanga a Jihohi 20 yayin da Tinubu zai Yi Murnar Ranar Dimokuradiyya

  • Ƙungiyar Take It Back Movement ta tabbatar da shirin gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 12 ga Yuni a jihohi akalla 20 na Najeriya
  • Zanga-zangar na da nufin nuna adawa da tsadar rayuwa, rashin tsaro da kuma tauye ‘yancin faɗar albarkacin baki a kasar nan
  • Ƴan zanga-zangar za su taru a wurare da dama ciki har da Eagle Square a Abuja, Toll Gate a Lagos da sauran wurare a Arewa da Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar masu fafutukar juyin siyasa a Najeriya mai suna Take It Back Movement, ta tabbatar da shirinta na gudanar da gagarumar zanga-zangar lumana.

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun bayyana cewa za su yi zanga zangar ne a ranar Ranar Dimokuraɗiyya, 12 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

Matasa sun fito zanga zangar goyon bayan Tinubu a Benue

Za a yi zanga zanga a Najeriya
An shirya zanga zanga a jihohi 20. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda za a gudanar da zanga zangar ne a shafin X na tsohon dan takarar shugaban kasa, Yele Sowore.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa zanga-zangar na da nufin tunkarar tsadar rayuwa, yawaitar rashin tsaro da kuma wasu ƙorafe korafe kan gwamnatin Bola Tinubu.

An samu bayanai kan yadda zanga zangar za ta gudana ne daga bakin mai tsara shirye shiryen ƙungiyar, Juwon Sanyaolu.

Tun a 2018 ne gwamnatin Muhammadu Buhari ta ayyana 12 ga Yuni a matsayin ranar Dimokuraɗiyya domin girmama marigayi Moshood Abiola, wanda ake ganin ya lashe zaɓen 1993.

Wuraren zanga zanga a Najeriya

Juwon Sanyaolu ya bayyana cewa an ware manyan wurare a jihohi fiye da 20 da za a gudanar da zanga-zangar.

Ya ce:

“A Abuja, za a taru a Eagle Square da misalin ƙarfe 8:00 na safe. A Legas kuma akwai wurare huɗu: Badagry, Maryland, Agbara da Toll Gate, duk za a fara da ƙarfe 7:00 na safe.”

Kara karanta wannan

An cafke matar babban alkali a Sokoto, ana zargin ta ci zarafin karamar yarinya

Sauran jihohi kuwa za a gudanar da gangami kamar haka:

  • Akure, Ondo: Kwanar Cathedral 8:00 na safe.
  • Benin, Edo: Gidan tarihi, 9:00 na safe.
  • Minna, Niger: Gidan Matasa, 8:00 na safe.
  • Damaturu, Yobe: Maiduguri Bypass, 7:30 na safe.
  • Ibadan, Oyo: Shataletalen Mokola, 8:00 na safe.
  • Bauchi: Gaban Makarantar ACR a Yelwa 8:00 na safe.
  • Osogbo, Osun: Kwanar Olaiya.
  • Yola, Adamawa: Hanyar Juppu Jam, 8:00 na safe.
  • Maiduguri, Borno: Kasuwan Gamboru, 8:00 na safe.
  • Kano, Kwanar Freedom Sharada

Bukatun masu zanga zanga a Najeriya

Ƙungiyar ta bayyana cewa zanga-zangar ta na nufin ƙara matsa lamba ga gwamnati domin mutunta dimokuraɗiyya da cika alkawura ga al’umma.

Masu zanga zanga sun ragargaji Tinubu
Masu zanga zanga zanga sun ce Tinubu ya gaza. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sanyaolu ya ce:

“Ranar 12 da Yuni dama ce ta ƙara tunatar da gwamnati cewa ‘yancin jama’a da tsaron su ne mafi girman nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata – abin da wannan gwamnati ta kasa yi.”

Legit ta tattauna da Musa Adamu

Legit ta tattauna da wani matashi a jihar Kano, Musa Adamu kan zanga zangar da aka ce za a yi a jihar.

Kara karanta wannan

Jerin hadiman Tinubu da suka ajiye mukami a shekara 2 da hawansa mulki

Musa ya ce:

"Na wuce ta wajen amma banga alamar mutane sun hadu domin zanga zangar ba, watakila su iya taruwa bayan wucewa ta.
"Watakila barnar da aka yi da kama mutane zuwa Abuja a wancan karon na cikin abin da ya hana mutane fitowa a yanzu."

An nemi 'yan Najeriya su yi hakuri da Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wani sarki a jihar Osun, Oba Abdulrashid Akanbi ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da Bola Tinubu.

Oba Akanbi ya ce duk da akwai tarin matsaloli a Najeriya, shugaba Tinubu ya dauko hanyar gyara da ya kamata ya cigaba.

Sarkin ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi hakuri su marawa Tinubu baya a 2027 domin cigaba da ayyukan raya kasa da ya fara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng