Gwamnatin Tinubu Ta Duba Matasa, Za a Yi Wa Mutane 100,000 Gata duk Shekara

Gwamnatin Tinubu Ta Duba Matasa, Za a Yi Wa Mutane 100,000 Gata duk Shekara

  • Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da 'Investonaire Academy' domin horas da matasa 100,000 duk shekara
  • Ministan matasa, Ayodele Olawande ya ce matakin zai koya wa matasa dabarun kasuwanci na zamani, da horo kan ilimin kuɗi da dabarbaru
  • Dr. Enefola Odiba na 'Investonaire Academy' ya ce shirin zai ƙarfafa matasa wajen yin tasiri a tattalin arziki ta hanyar samun ilimi da ƙwarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya ba matasan Najeriya horo na musamman domin dogaro da kansu.

Gwamnatin Tinubu ta yi yarjejeniya da 'Investonaire Academy' domin koyar da matasa 100,000 duk shekara kan cinikayyar kuɗin ƙetare don rage rashin aiki.

Gwamnatin Tinubu za ta horas da matasa 100,000
Gwamnatin Tinubu ta shirya horas da matasa 100,000 duk shekara. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

An shirya ba matasan Najeriya horo na musamman

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa ranar Talata da daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar matasa, Omolara Esan, ya sanya wa hannu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Dattawan Arewa sun dira a kan masu tallata Tinubu tun yanzu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarjejeniyar da aka kulla a ranar Litinin a Abuja, za ta ba matasa horo a harkokin 'forex trading', kula da matsalolin kudi da asara da kuma fahimtar harkokin kuɗi.

Da yake magana, Ministan matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana shirin a matsayin mataki mai muhimmanci wajen ƙarfafa matasa da fasahar zamani.

Ya ce:

“Ina ganin wannan haɗin gwiwa a matsayin hangen nesa mai zurfi don cigaban matasa, ba wai ciniki kawai ba, muna koyar da tunani mai zurfi.
“Muna koya musu amfani da na’urorin zamani da yadda za su cinye dama a duniya domin gina dukiya da bunƙasa ƙasa.”

Sanarwar ta ce Ministan ya jaddada cewa a lokacin da tattalin arziki ke fuskantar ƙalubale, irin waɗannan shirye-shirye na da muhimmanci ga samun ‘yancin kuɗi.

“Ina so in jaddada cewa wannan yarjejeniya ba wai shiri ne kawai ba, za mu tabbatar da inganci da sakamako na ainihi.

- Cewar ministan matasa

Kara karanta wannan

Dangote zai girgiza harkar man fetur da manyan sauye sauye a Najeriya

Tinubu zai yi wa matasan Najeriya gata
Gwamnatin Tarayya ta shirya yi wa matasa gata a Najeriya. Hoto: Ayodele Olawande.
Source: Twitter

Musabbabin shirya horon ga matasan Najeriya

A nasa ɓangaren, daraktan shirye-shiryen na Investonaire Academy, Dr. Enefola Odiba, ya ce shirin zai haɓaka ilimi da ƙarfin tattalin arzikin matasa.

Ya ce:

“Matasa ginshikin kowace ƙasa ne, idan an ba su ƙarfi, su ke zama tushen cigaba da kirkire-kirkire, wannan shiri zai inganta rayuwar matasa."

Odiba ya ƙara da cewa shirin yana da nasaba da ƙoƙarin gwamnati na ɗora matasa a kan hanyar cigaban fasaha da bunƙasa tattalin arziki.

Ma’aikatar ta kuma sake jaddada aniyarta wajen aiwatar da shirin cikin gaskiya, inganci da sakamakon da zai bayyanu, don ciyar da matasa gaba.

Gwamnatin Tinubu ta raba tallafi ga al'umma

Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ba mutane miliyan shida tallafin kudi cikin wata shida da suka gabata a Najeriya domin rage halin kunci.

Ministan jin kai d walwala, Nentawe Yilwatda ya ce an cire bayanan karya daga rajistar tallafi, an kuma fara amfani da fasahar zamani don tabbatar da cancanta.

Nentawe ya ce shugaban kasa ya umurci a ba gidaje miliyan 15 tallafin kudi kafin watan Oktoba, tare da hadin gwiwa da Bankin Duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.