Bayan Gama Hutun Sallah, Tinubu Ya Dura Abuja, Ya Kaddamar da Wani Babban Aiki
- Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan shafe kwanaki 13 a Legas, inda ya halarci bikin ECOWAS tare da hutun babbar Sallah
- A Legas, an ce Shugaba Tinubu ya karbi baki tare da kaddamar da ayyukan tituna, ciki har da babban titin gabar teku na Legas-Calabar
- Yayin da ya dura Abuja a ranar Talata, an ce Tinubu zai kaddamar da ginin cibiyar ICC a jerin ayyuka 17 da Nyesom Wike ya kammala
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan shafe kwanaki 13 a Legas, inda ya halarci bikin cika shekaru 50 na kungiyar ECOWAS da kuma bikin babbar Sallah.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 2:10 na rana.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Legas
Yayin zamansa a Legas, Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin manyan baki daban-daban kuma ya kaddamar da ayyuka da dama don murnar cikarsa shekaru biyu a kan mulki, inji rahoton shafin State House.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 31 ga Mayu, 2025, ya kaddamar da muhimman ayyukan tituna a Legas, ciki har da sashen farko na babbar hanyar teku ta Legas-Calabar.
Sauran ayyukan sun hada da titin zuwa tashar tsandauri ta Lekkki, tare da kuma kaddamar da fara aikin sashe na biyu na hanyar Legas-Calabar da kuma hanyar 7th Axial.
Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Arewa
Bugu da kari, Shugaban ya kaddamar da wasu ayyukan tituna ta hanyar kafar bidiyo a Arewacin Najeriya.
Wadannan ayyukan sun hada da sashe na biyu na titin Kano-Kanwar-Danja-Hadejiya, titin Yakasai-Zalli, da kuma babbar hanyar Arewacin Kano.
Wadannan ayyuka sun nuna fifikon gwamnatin Tinubu kan samar da ababen more rayuwa don bunkasa tattalin arziki.
Bayan isowarsa filin jirgin saman Abuja a ranar Talata, sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, da shugaban ma’aikata, Hon. Femi Gbajabiamila, tare da sauran manyan jami'an gwamnati, sun tarbi Tinubu.

Source: Twitter
Tinubu ya kaddamar da ICC a Abuja
Nan take ya wuce daga filin jirgin sama zuwa cibiyar taro ta kasa da kasa (ICC) don kaddamar da kayataccen ginin cibiyar, wani aikin da ma’aikatar FCTA ta gudanar, inji rahoton The Nation.
Kaddamar da cibiyar ICC a ranar 10 ga Yuni ya nuna fara shirin kaddamar da ayyuka na kwanaki 17 a Abuja, kamar yadda ministan FCT, Nyesom Wike, ya sanar.
Sake gina cibiyar ICC na daga cikin ayyuka 17 da aka kamalla, kuma Tinubu zai kaddamar da guda 10 yayin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai kaddamar da sauran.
Sauran ayyukan sun hada da titin Pai-10 a karamar hukumar Kwali, hanyar shiga kwalejin yaki ta Ushafa a Bwari, hanyar shiga Gishiri da gada da ke hada Jahi da Maitama, da kuma titin Wole Soyinka/Murtala Muhammad.
Tsohon gwamnan Ekiti ya gana da Tinubu
Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Legas domin taya shi murnar babbar Sallah.
Ayodele Fayose ya shaida cewa ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu domin jinjina masa kan yadda yake kokarin ceto Najeriya daga durkushewar tattalin arziki.
Hakazalika, ya shaida cewa ba zai taba barin jam'iyyar PDP zuwa APC ba, duk da cewa yana goyon bayan Tinubu tun lokacin da yake kan kujerar gwamnan Ekiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


