Tashin Hankali a Abuja Yayin da Aka Yi Harbe-Harbe a Kusa da Cibiyar Taro Ta Kasa da Kasa
- Rahoto sun nuna cewa an yi harbe-harbe a kusa da cibiyar taro ta kasa da kasa da ke babban birnin tarayya Abuja
- Hakan na zuwa ne yayin da ake zaben sabbin shugabanni na kungiyar dalibai ta kasa (NAN) a yau Juma'a, 1 ga watan Disamba
- Zuwa yanzu hanyar da ke sada mutum da cibiyar taron ya zama ba kowa yayin da yan sanda suka harba barkonon tsohuwa don tarwatsa jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Zaben kungiyar daliban Najeriya na kasa (NANS) na gudana a yanzu haka a babbar cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Abuja inda za su zabi sabbin shugabanni, rahoton The Nation.
Kamar yadda TVC News ta rahoto, an yi harbe-harbe a kusa da babbar cibiyar taron na kasa da kasa a babban birnin tarayya.
Yan sanda sun tarwatsa jama'a
Domin tsoron kada harbi ya same su, rundunar yan sanda ta harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa taron jama'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa babban hanyar da ke sada mutum ga cibiyar taron ya zama ba kowa a yanzu sakamakon harbe harben da aka yi.
Kungiyar NANS ta kira zanga-zanga
A wani labari na daban, Legit Hausa ta kawo a baya cewa kungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta yi kira ga ɗalibai da su shirya gudanar da zanga-zanga kan ƙarin kuɗin makarantun gaba da sakandire da aka yi a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin jami'o'in gwamnatin tarayya da na jihohi sun ƙara kuɗin makarantarsu fiye da kaso 100%, yayin da aka ƙara kuɗin makarantun 'Unity Schools' na gwamnatin tarayya daga N45,000 zuwa N100,000.
Ƙungiyar NANS a cikin wata sanarwa da kakakinta na ƙasa, Giwa Temitope, ta fitar ta nuna rashin dacewar ƙarin kuɗin makarantar da gwamnati ta yi, cewar rahoton The Punch.
Jami’an NSCDC sun harbi dalibai a Abuja
A gefe guda, mun kuma ji a baya cewa rundunar yan sanda ta kama tare da tsare wasu jami'an hukumar NSCDC guda uku a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba kan harbin wasu dalibai biyu a makarantar sakandare na Life Camp.
Makarantar na a tsakanin yankunan Jabi da Gwarinpa a babban birnin tarayya, Abuja.
Asali: Legit.ng