Ministan Tinubu Ya Faɗi Mutum 1 da Zai Yi Wa Biyayya bayan Allah a Rayuwarsa

Ministan Tinubu Ya Faɗi Mutum 1 da Zai Yi Wa Biyayya bayan Allah a Rayuwarsa

  • Ministan ayyuka a Najeriya, David Umahi, ya yi magana kan salon mulkin Shugaba Bola Tinubu da ayyukan alheri da yake yi
  • Tsohon gwamnan na Ebonyi ya ce bayan biyayya ga Allah, babu wanda ya cancanci haka sai Bola Tinubu saboda amincewa da shi
  • Umahi ya ce yabon da Shugaba Tinubu ya masa yana da daraja fiye da $1trn idan za a kwatanta farin cikin da ya yi dalilin haka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT Abuja - Ministan Ayyuka, David Umahi, ya jaddada biyayyarsa da Shugaba Bola Tinubu duba da irin salon shugabancin da yake yi.

Umahi ya ce bayan Allah, Shugaba Bola Tinubu ne ke gaba a wajen biyayya da amana da ya kamata a ba shi.

Minista ya yabawa Tinubu kan ayyukan alheri
Ministan ayyuka, Umahi ya ji dadin yabon da Tinubu ke masa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da Bola Tinubu ya yi wa Umahi

Kara karanta wannan

Zamfara: Bello Turji ya kawo sabon salo, ya gindaya sharuɗan yin noma a bana

Umahi ya bayyana hakan ne a Abakaliki yayin da yake magana da manema labarai, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce ya ji dadi kan yadda shugaban kasa ya yaba masa game da ayyukan ci gaba da ya gudanar.

Tsohon gwamnan ya ce yabon da shugaban ya masa ya fi darajar $1trn a gare shi, domin yana tabbatar da cewa yana kan turba mai kyau.

Ya ce:

"Na sha fada wa shugaban kasa, har a bainar jama’a, cewa biyayyata tana ga Allah da shi.
"Idan mutum ya ba ka amana irin ta Tinubu, to za ka zama shaidani idan ka ci amanarsa."

Umahi ya gargadi masu cin amanar Tinubu

Umahi ya ce duk wanda ya ci amanar Tinubu bayan samun irin wannan amana da goyon baya, zai fuskanci fushin Allah.

"Ka taɓa ganin inda mutum ya jagoranci sayan kayan aikin da kudinsa ya kai N1.6trn kuma shugaban ba ya tambayarsa yadda ya yi?"
"Magana nake kan wani ɓangare na aikin, dangane da tsawonsa. Ina addu’a kullum cewa idan na fifita kaina, iyalina ko abokai sama da Allah, Tinubu da ‘yan Najeriya, to ka da Allah ya karɓi addu’ata."

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya ajiye aiki, ya fadi dalilin rabuwa da gwamnatin APC

- Cewar Umahi

Minista ya fadi abin Tinubu ya yi masa na karramawa
Ministan ayyuka, Umahi ya yabawa Bola Tinubu kan ayyukan alheri. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Alƙawarin da Umahi ya yi wa Tinubu

Umahi ya sha alwashin ci gaba da yin addu’a ga Tinubu da duk masu ƙaunarsa da yabawa abubuwan da yake yi wanda yake kawo cigaba a Najeriya, cewar Punch.

Ya kara da cewa:

"Na sadaukar da yabon shugaban kasa ga dukkan masu roƙon nasarata wajen hidimtawa al’umma."
"Yana nufin ‘yan kwangila za su farka domin kammala manyan ayyuka kusan 30 da shugaban zai kaddamar kafin 20 ga watan Disamba."
"Ni nake da alhakin ginawa da duba ayyukan da suka bazu a dukkan shiyyoyin ƙasar nan guda shida."

Umahi ya roki Musulmi su goyi bayan Tinubu

A baya, kun ji cewa ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya yi buɗa baki tare da al'ummar Musulmai a gidansa da ke jihar Ebonyi.

David Umahi ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga al'ummar Musulmai su marawa shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Tsohon gwamnan na jihar Ebonyi ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu yana da kyakkyawar manufa kan ci gaban Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.