Dakarun Sojoji Sun Hallaka Shugaba a Kungiyar ISWAP, an Kwato Makamai
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun addabi ƴan ta'adda da kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin sun samu nasarar hallaka wani shugaba a cikin ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP mai suna Mallam Jidda yayin wani artabu da suka yi a jihar Yobe
- Hakazalika, dakarun sojojin sun kashe ƴan ta'adda masu tare da ƙwato makamai da dama a wani kwanton ɓauna da suka shirya musu a jihar Borno
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Dakarun sojojin Najeriya sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan ƴan ta’addan ISWAP a yankin Arewa maso Gabas.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe wani babban kwamandan ƴan ta’addan ISWAP tare da ƙwato makamai iri-iri a wasu hare-hare na musamman.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kashe shugaba a ISWAP
Dakarun sojojin sun kai wani farmaki na musamman a ƙauyen Ngazalgana, ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe, inda suka yi arangama da ƴan ta’adda.
Sojojin sun kuma kashe Malam Jidda, wanda aka bayyana a matsayin shugaba (Ameer) na ƙauyukan Ngorgore da Malumti.
Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun sun ƙwato makamai daga hannun kwamanda nda aka kashe, ciki har da bindigogin AK-47, jigida da babur da ƴan ta’addan ke amfani da shi wajen tafiye-tafiye.
“A wani hari daban a yankin Timbuktu Triangle, dakarun sojoji waɗanda suka shirya kwanton ɓauna sun yi artabu da wasu mayaƙan ISWAP."
"An kashe wasu daga cikin ƴan ta’addan, sannan sojoji sun ƙara ƙwato bindigogin AK-47 da wasu nau’ikan makamai daban-daban."
- Wata majiya
Sojoji sun gano gawarwakin ƴan ta'adda
Haka nan a yankin Abadam da ke Arewacin Borno, dakarun da ke gudanar sintiri bayan wata arangama da suka yi a Mallamfatori sun ci gaba da gano gawarwakin ƴan ta’adda da kuma makaman da suka ajiye yayin tserewa.

Source: Original
"Ƴan ta’addan sun gudu cikin rikicewa, suna barin makamai iri-iri bayan gagarumar ƙawanya da dakarun sojoji suka yi musu."
- Wata majiya
Wannan gagarumar nasara na cikin ƙoƙarin haɗin gwiwa da rundunar sojojin Najeriya ke yi domin tarwatsa sansanonin ƴan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa a fadin Arewa maso Gabas.
Abin a yaba ne
Abubakar Salisu ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da dakarun sojojin suka samu abin a yaba ne.
"Gaskiya sun nuna bajinta kuma muns yaba musu sosai kan nasarar da suka samu. Muna matuƙar jin daɗi idan muka samu labarin kashe ƴan ta'adda."
"Muna addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara a kan ƴan ta'adda."
- Abubakar Salisu
Batun harin ƴan ta'adda kan Janar Buratai
A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi ta yaɗa wasi rahotanni masu cewa tsohon babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya fuskanci harin kwanton ɓauna daga wajen ƴan ta'addan Boko Haram.

Kara karanta wannan
Benue: 'Yan bindiga sun shiga gida gida da tsakar dare, sun yi wa bayin Allah kisan gilla
Labaran sun nuna cewa Janar Buratai ya tsallake rijiya da baya a harin da ƴan ta'addan suka kai masa a kusa da wani sansanin sojoji.
Sai dai, ko kaɗan ba haka lamarin yake ba, domin ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram ba su yi wa Janar Buratai kwanton ɓauna ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

