Hare Haren 'Yan Bindiga Sun Dauke Hafsan Sojojin Kasa daga Abuja zuwa Benue
- Hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Oluyede, ya koma Makurdi domin jagorantar dakarun da za su dakile hare-haren ‘yan ta'adda a Benue
- Rahotanni sun nuna cewa an kashe fiye da mutum 300 cikin watanni biyu a Benue, inda aka kona gidaje da korar jama’a daga kauyukansu
- Oluyede zai duba sansanonin soji kuma ya gana da jami’ai da jama’ar kauyauka, domin ƙarfafa gwiwar sojoji da tabbatar da tsaro a fadin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - A wani mataki mai jan hankali, hafsan hafsoshin sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya koma Makurdi, babban birnin jihar Benue.
An rahoto cewa Laftanar Janar Olufemi ya koma Makurdi bayan karuwar hare-haren makiyaya da ‘yan bindiga da suka yi silar mutuwar daruruwan mutane.

Source: Facebook
Shugaban sojojin kasa ya koma Benue

Kara karanta wannan
Sojoji sun ƙara samun matsala, jirgin yaƙi ya yi kuskuren sakin wuta a jihar Zamfara
Majiyoyin soja sun tabbatar cewa Oluyede ya bar Abuja da safiyar Talata tare da wasu manyan hafsoshin rundunar sojin kasa, a cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laftanar Janar Oluyede zai gudanar da rangadi da kuma tsara yadda za a dakile hare-haren da gwamnatin jihar ta ce ana kai wa jama'a kusan kullum.
Wani babban jami'in soja da ya nemi a sakaya sunansa ya bayya cewa:
"An tura wasu sababbin dakarun soja zuwa Benue domin su taimaka wajen fatattakar mahara tare da dawo da doka da oda a jihar."
An kashe sama da mutane 300 a Benue
'Yan bindiga sun kara kaimi wajen kai hare-hare a garuruwan jihar, suka kashe daruruwan mutane, suka kori mutane daga garurunsu tare da kona gidaje da dama.
Rahotannin da aka tattara sun nuna cewa 'yan ta'addar da suka hada da 'yan bindiga da makiyaya sun kashe sama da mutane 300 a cikin watanni biyu da suka wuce.
Gwamna Hyacinth Alia ya tabbatar da wadannan sababbin jerin hare-haren yayin wani taron tsaro da aka yi a Makurdi.
“An kashe mutum 12 a karamar hukumar Apa, sannan an gano gawarwaki 11 a Gwer ta Yamma,” inji Gwamna Alia.

Source: Twitter
Amfanin komawar shugaban sojojin Benue
A ziyarar tasa, ana sa ran hafsan sojan zai gana da kwamandojin soji, ya kuma kai ziyarar gani da ido sansanonin sojin jihar da kuma tattaunawa da jama’ar da lamarin ya rutsa da su.
Majiyoyin soja sun ce manufarsa ita ce “kara wa sojoji kwarin gwiwa” da tabbatar wa da mazauna yankin cewa sojoji na bakin kokarinsu wajen ba su kariya, inji rahoton NTA.
Hare-haren baya bayan nan sun tayar da kura a fadin Najeriya, inda wasu ke fassara su a matsayin yunkurin kisan kare dangi na kabilu.
Ko a ranar Asabar da ta gabata, sai da aka sace 'yan kasuwa 14 da ke tafiya a cikin motar haya ta Benue Links a kan titin Owukpa, inda har yanzu ba a san inda suke ba.
'Yan bindiga sun kashe mutane 43 a Benue
A wani labarin, mun ruwaito cewa, aƙalla mutum 43 ne suka rasa rayukansu a harin da 'yan bindiga suka kai kauyukan Gwer ta Yamma da Apa a jihar Benue.
Maharan sun farmaki garuruwan Tse Antswam da Edikwu Ankpali, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 43.
Hukumomi sun tabbatar da faruwar lamarin tare da gudanar da bincike don kamo maharan, yayin da ake cigaba da neman wasu da suka bace a harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

