Gwamna Dauda Lawal Ya Faranta Ran Ma'aikata yayin da Ake Shirin Bikin Sallah
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince a fitar da kuɗaɗe don biyan ma'aikata da ƴan fansho saboda bukukuwan Sallah
- Dauda Lawal ya amince a ba da kuɗaɗen ne a matsayin alawus don ma'aikata da ƴan fansho su yi bukukuwan Sallah cikin walwala
- Tsohon ma'aikacin bankin ya kuma buƙaci a sanya jihar Zamfara cikin addu'a don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan kuɗi don bikin babbar Sallah (Eid-el-Kabir) ga ma'aikata.
Gwamna Dauda Lawal Dare ya amince da biyan kuɗin ne a matsayin alawus ga dukkan ma'aikata da ƴan fansho a faɗin jihar.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar Zamfara, Alhaji Mahmoud Muhammad Dantawasa, ya fitar a ranar Talata, 3 ga watan Yunin 2025, cewar rahoton jaridar Leadership.
Gwamna Dauda ya ba ma'aikatan Zamfara kuɗi
Ya bayyana cewa wannan kyauta ta kuɗi da gwamnati ta ware na da nufin rage wa iyalai nauyin rayuwa da su ke fuskanta, tare da ba su damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin annashuwa da walwala.
Gwamna Dauda Lawal, wanda yanzu haka yake ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji, ya aika da saƙon fatan alheri ga al’ummar jihar.
Ya roƙi jama’a da su yi bikin Sallah cikin lumana, natsuwa da kwanciyar hankali, tare da ci gaba da yi wa jihar addu’a domin samun zaman lafiya, ci gaba da kuma yalwar arziƙi, rahoton The Sun ya tabbatar.
“Na gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya ba mu ikon ganin wannan lokaci mai albarka na Babbar Sallah. Yayin da muke gudanar da bukukuwa, ina ƙarfafa gwiwar kowa da kowa da ya tuna da ma'anar wannan lokaci na haɗin kai, sadaukarwa, da jinƙai.
“Mu ci gaba da yi wa jihar Zamfara da ƙasarmu Najeriya addu’a. Tare da haɗin kai da ƙoƙari, za mu iya gina makoma mai albarka ga kanmu da kuma ga zuriyarmu ta gaba."
- Gwamna Dauda Lawal
Gwamna Dauda ya yi tunatarwa
Haka kuma, ya ja hankalin al’umma da su kasance masu kishin ƙasa da mutunta juna, su guji tayar da husuma a lokacin bukukuwan Sallah, su kuma taimaka wa marasa galihu da waɗanda ke cikin buƙata domin samun lada da albarka daga Allah.

Source: Twitter
Wannan biyan kuɗin ƙarin Sallah na daga cikin manufofin Gwamna Dauda Lawal na ganin ma’aikata da ƴan fansho sun samu kulawa yadda ya kamata.
Kyautar ta zo ne musamman a lokutan bukukuwa da ke buƙatar ƙarin kuɗi don gudanarwa cikin jin daɗi da farin ciki.
Wannan mataki ya jawo yabo daga al’umma, mutane da dama na bayyana godiya ga gwamnan bisa wannan kyakkyawan tanadi da nuna kulawa ga jin daɗin jama’a.
Gwamna Ahmed ya amince a biya albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince a biya ma'aikata albashi.
Gwamnan ya amince a biya albashin ne na watan Yunin 2025, domin ma'aikata su samu damar yin bukukuwan babbar Sallah cikin walwala.
Ya kuma buƙace su da ƙara jajircewa wajen sauke nauyin da ke kansu tare da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


