An 'Gano' Silar Tsadar Ragunan Layya yayin da Masu Sana'ar Suka Koka kan Rashin Ciniki
- 'Yan kasuwa masu sayar da raguna sun koka da rashin kasuwa yayin da farashin raguna ya karu da fiye da kasshi 85 a birnin Abuja
- Wasu masu siye sun ce rashin kudi da halin tattalin arziki ya hana su siyan raguna, inda wasu suka ce za su sayi kaji maimakon haka
- Masu sayar da raguna sun dora laifin hauhawar farashi kan rashin tsaro a Arewa da kuma shigo da raguna daga kasashen waje
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Kwana hudu kacal kafin bikin babbar sallah, farashin raguna ya karu da fiye da kashi 85 cikin 100 a yankunan Abuja.
Wannan yana faruwa ne yayin da masu sayar da raguna ke korafi kan rashin kasuwa, yayin da abokan hulda ke alakanta hauhawar farashin da yanayi tattalin arziki.

Kara karanta wannan
'Ni kaɗai zan yi': Sarki ya haramta layya saboda tsadar rayuwa, zai yi wa ƴan kasa

Source: Getty Images
'Yan kasuwa sun koka kan tsadar raguna
Binciken wakilin Daily Trust ya nuna farashin raguna ya wuce na bara sosai, inda mutane ke cewa ba za su iya siyan raguna ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kasuwar dabbobi da ke Unguwar Sabon Tasha a Abaji, ƙaramin rago da ake sayarwa N120,000 a bara, yanzu ya kai N200,000 zuwa N250,000.
Rago matsakaici da ake siyarwa N200,000 a bara, yanzu ya kai N270,000 zuwa N300,000; manya sun kai N450,000 zuwa har N1.2m.
An ji cewa a kasuwar Kwali, rago matsakaici da ake siyar da N120,000 bara, yanzu ya kai N180,000 zuwa N230,000; manya sun kai N550,000 zuwa N780,000.
A kasuwar Gwagwalada da ke kan hanyar Gwako-Giri-Abuja-Lokoja, raguna matsakaita sun kai N250,000 zuwa N300,000, manyan kuma har N750,000.
A kasuwar Kuje, raguna matsakaita daga N130,000 sun tashi zuwa N260,000; manya daga N250,000 zuwa N450,000.
Dillalan raguna sun yi tagumi a Abuja
Masu sayar da raguna sun koka da rashin kasuwa a yawancin kasuwanni da aka samu rahotanni a babban birnin tarayya.
Wasu daga cikinsu sun ce abokan huldarsu na gudu ne saboda hauhawar farashin raguna da kuma matsin tattalin arziki da ake ciki.
Malam Garba Shehu, ɗan kasuwa a Zuba, ya ce ya kawo raguna 120, amma ya sayar da 11 kacal cikin mako guda.
Wani ɗan kasuwa Kabiru Ibrahim ya ce ya kawo raguna 135 daga Sokoto, amma cikin sati guda, ya sayar da ɗaya kacal.
Ya ce:
“Yanzu haka, mako guda kenan da na kawo wadannan raguna, amma kwastomomi na jin farashi sai su juya ba su dawo ba."
Ya ce masu saya da ya saba da su a baya yanzu ba sa iya siyan rago saboda karancin kudi da matsin rayuwa.

Source: Original
Babbar sallah: An fadi silar tsadar dabbobi
Wasu yan kasuwa sun ce hauhawar farashi ya samo asali ne daga matsalolin tsaro a Arewa da ya hana shigo da dabbobi.
Sun ce rashin tsaro ya tilastawa wasu yan kasuwa shigo da raguna daga kasashen Mali, Nijar da Chadi, wanda hakan ke kara farashi.
“Ka sani a matsayin dan jarida, rashin tsaro a Arewa yana ta kara muni, ana sace dabbobi da kashe masu kiwo."
Ya kara da cewa karancin dabbobi da rashin abokan hulda na sa raguna su yi tsada, domin mutane da dama ba su da isasshen kudi.
Mota dauke da ragunan layya ta yi hatsari
Mun ba ku labarin cewa wata mota ɗauke da raguna da shanu domin bukukuwan babbar salla ta yi hatsari.
Motar ta gamu da mummunan hatsarin ne a jihar Osun kamar yadda Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar.
Hukumar reshen jihar Osun ta tabbatar da cewa mutum biyu sun mutu, wasu 15 sun samu raunuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

