'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan jami'an rundunar CJTF da ke aikin samar da tsaro a jihar Zamfara
  • Miyagun sun hallaka wasu daga cikin jami'an CJTF a harin da suka kai musu a ƙaramar hukumar Kaura-Namoda
  • A yayin arangamar da aka yi a tsakanin ɓangarorin guda biyu, an kashe wasu daga cikin tsagerun ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun yi wa jami'an rundunar CJTF kwanton ɓauna a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kashe mambobi biyu na CJTF tare da wani mamba 'dan rundunar Askarawan Zamfara a yayin harin.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun kashe jami'an CJTF a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin kwanton ɓaunan ya faru ne a ranar Asabar a kan hanyar Gusau zuwa Kaura Namoda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika an kuma yi garkuwa da mutane da dama a ranar a kan hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka babban kwamandan Boko Haram da mayaka masu yawa

Yadda ƴan bindiga suka farmaki jami'an CJTF

Majiyoyi sun bayyana cewa an kawo jami’an CJTF daga Maiduguri ne domin taimakawa wajen daƙile hare-haren da ke ci gaba da faruwa a ƙaramar hukumar Kaura Namoda.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da waɗanda suka taimaka wajen turo su ba.

Wani mazaunin Kaura Namoda, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce harin farko ya faru ne a wani wurin shingen binciken CJTF da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

“Ɗaya daga cikin jami’an CJTF ya rasa ransa a lokacin harin. Bayan haka, sauran jami’an da Askarawan Zamfara sun bi sahun maharan, ba tare da sanin cewa sun shirya musu kwanton ɓauna ba."

- Wata majiya

Fafatawar da ta biyo baya ta yi sanadiyyar mutuwar wani jami’in CJTF da mamban Askarawan Zamfara guda ɗaya.

Majiyar ta ƙara da cewa rahotanni da ba a tabbatar ba sun nuna cewa akwai yiwuwar an kashe ƴan bindiga guda biyar a yayin arangamar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane sama da 100 bayan kai mummunan hari Kebbi

Wata majiya ta ce jami’an CJTF sun kutsa cikin maɓoyar ƴan bindigan, kuma sun fara samun nasara kafin harsashinsu ya ƙare.

“Yayin da suke janyewa, sai suka tsinci kansu a cikin wani kwanton ɓauna inda aka kashe uku daga cikinsu."

- Wata majiya

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Zamfara
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Zamfara Hoto: Legit.ng
Source: Original

Abin da ƴan sanda suka ce kan harin

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce bai da masaniya game da harin amma ya yi alƙawarin bincike don bayar da bayani.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga gare shi ba.

Tuni aka riga aka birne mamatan bisa ga koyarwar addinin Musulunci.

Ƴan bindiga sun kai hari a masallaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a wani masallaci da ke jihar Zamfara.

Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da masallata a harin da suka kai lokacin da ake tsuga ruwan sama.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙaramar hukumar Anka lokacin da ake yin Sallar Isha'i.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng