"Ko Sisin Kobo": Gwamna Uba Sani Ya Fadi Yadda Ya Kaucewa Ciyo Bashi a Kaduna
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa tun hawansa kan karagar mulki, bai karɓo bashin ko sisin kobo ba har yau
- Uba ya ce ya ƙi yarda da tayin da wasu cibiyoyin kuɗi suka yi masa na karɓar lamuni, saboda baya son ƙara ɗorawa jihar nauyi
- Ya bayyana cewa ya ɗauki matakin rage alawus na wasu manyan jami'an gwamnatinsa domin rage kuɗaɗen da ake kashewa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan ciyo basussuka bayan hawansa mulki.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa tun da ya hau mulki shekaru biyu da suka wuce, bai karɓi wani bashi daga kowace cibiyar kuɗi ta cikin gida ko ta ƙasa da ƙasa ba.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyin wasu ƴan jarida a wani ɓangare na shagulgulan cika shekaru biyu a mulki, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Uba Sani ya ƙi ciyo bashi a Kaduna
A cewarsa, bankuna da dama sun nemi ya karɓi bashi ta hanyoyi daban-daban, amma ya ƙi amincewa da su domin ba ya son jefa jihar cikin ƙarin bashi.
Gwamnan ya bayyana cewa ya rage alawus da ake ba wa sakataren gwamnatin jiha da kwamishinoni domin gudanar da mulki cikin tsari da tattali, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
“Sakataren gwamnatin jiha tsohon babban sakatare ne a matakin tarayya, wanda kuma ya taɓa aiki da hukumar abinci da noma ta majalisar ɗinkin duniya (FAO). Wasu daga cikin Kwamishinonin kuma suna karɓar albashi mai tsoka a wuraren da suka yi aiki a baya."
"Na roƙesu su haƙura da alawus da ake basu, kuma su ci gaba da amfani da tsofaffin motocin da waɗanda suka gabace su suka bari. Haka ne yadda muke tafiyar da gwamnati ba tare da karɓar ko sisin kwabo na bashi ba."
- Gwamna Uba Sani
Wane hanyoyi Uba Sani yake samo kuɗi?
Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa ya yi amfani da sanayyar da ya yi wa mutane a cikin shekarunsa na gwagwarmaya da aikin majalisa domin jawo tallafi daga ƙungiyoyin bayar da agaji.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa gidauniyar Qatar Charity na gina Kaduna Economic City tare da aiwatar da aikin gidaje masu yawa a Millennium City, yana mai cewa gine-ginen na dab da kammaluwa.
Gwamna Uba Sani ya kuma yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa taimakon da yake ba jihar Kaduna, kamar yadda yake taimakawa sauran jihohin Najeriya domin fuskantar ƙalubalen kuɗi.
Uba Sani ya magantu kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan rashin da ake fama da ita a Arewacin Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya bayyana talauci na daga cikin manyan dalilan da suke kawo matsalar rashin tsaro a yankin Arewa.
Uba Sani ya bayyana cewa yankin Arewa zai ci gaba da fuskantar rikice-rikice har idan ba a shawo kan matsalar ta hanyar da ta dace ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

