Bayan Yanke Mata Hukunci, Kotu Ta Umarci a ba Jarumar TikTok, Murja Kunya Muƙami a CBN
- Kotu ta yanke wa shahararriyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya hukuncin ɗaurin watanni shida ko biyan tara N50,000
- Simone Amobeda ya yanke wa Murja Kunya wannan hukunci ne bayan kama ta da laifin likin kudi da tattake su a otal wanda ya saba doka
- Alkalin ya kuma umarci a naɗa Murja Kunya matsayin jakadar CBN da EFCC wajen wayar da kan jama'a illar wulaƙanta takardun kudi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Babbar Kotun Tarayya mai zama a Kano ta yanke wa fitacciyar ƴar TikTok,, Murja Ibrahim Kunya, hukuncin daurin watanni shida ko zaɓin biyan tarar N50,000.
Kotun karƙashin jagorancin Mai shari'a Simone Amobeda ta yanke wa Murja Kunya wannan hukuncin bayan kama ta da laifin wulaƙanta takardun Naira.

Source: Facebook
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi watau EFCC ta tabbatar da hukunta Murja a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC cafke jarumar TikTok ɗin ne bisa zargin liƙi da Naira da tattake su yayin rawa a ɗakin otal na Guest Palace da ke Kano, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wane laifi Murja Kunya ta aikata
Murja ta aikata laifin ne a watan Disamba, 2023, wanda ya saɓawa dokar Sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta 2007.
A watan Janairu 2025, EFCC ta kama ta bisa zargin karya wannan doka, amma an bayar da ita belin ofis yayin da ake shirin gurfanar da ita a gaban kotu.
Duk da haka, Murja Kunya ta tsere lokacin da aka bukaci ta bayyana a gaban kotu domin ci gaba da shari’a.
Yadda EFCC ta sha fama da Murja Kunya
Bayan wasu makonni na bincike da sa ido, jami’an EFCC suka samu nasarar sake kama ta a ranar Lahadi, 16 ga Maris, 2025.
Daga nan aka sake gurfanar da ita a ranar 20 ga Mayu, inda ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi.

Kara karanta wannan
"Ba ɗan ƙunar baƙin wake ba ne," Ministan Tinubu ya gano mutumin da ya tashi 'bam' a Abuja
Bayan lauyan EFCC, Musa Isah ya gabatar da hujjoji, kotu ta yanke mata hukuncin zaman gidan yari na watanni shida ko kuma ta biya tarar N50,000.

Source: Facebook
Wane muƙami za a ba Murja Kunya a CBN?
A wani bangare da ke dauke da manufar gyara, alkali ya ba da umarnin a nada Murja Kunya a matsayin Jakadar CBN da EFCC a kamfen wayar da kan jama'a illar wulaƙanta Naira.
Hukuncin ya bukaci ta yi amfani da shahararta a TikTok da sauran kafafen sada zumunta wajen fadakar da mabiyanta kan muhimmancin girmama kudin Najeriya da illar wulaƙanta su.
Wannan hukunci ya zamo na farko da aka yanke wa wani fitacce a kafafen sada zumunta dangane da sabawa dokar kare ƙimar Naira.
Kotu ta ɗaure ɗan TikTok watanni 6 a kurkuku
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya mai zama a Kaduna ta yanke wa wani matashin ɗan TikTok, Muhammad Kabir hukuncin ɗauri a gidan yari.
Kotun ta ɗaure fitaccen ɗan TikTok din ne sabida cin zarafin takardun Naira a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa.
Kotu ta yanke masa hukuncin daurin watanni shida ko zabin biyan tarar N300,000 ga gwamnatin tarayya bisa laifin take kudin Najeriyan.
Asali: Legit.ng
