Rufe Matatar Fatakwal bayan Ta Laƙume Dala Biliyan 1.5 da Martanin Masana a Najeriya
Rivers - Sanarwar rufe matatar man fetur ta Fatakwal da ke jihar Ribas a Kudancin Najeriya ta jawo ce-ce-ku-ce da martani mai zafi daga masana da ƴan ƙasa.
Masana harkokin man fetur sun dage cewa ya kamata gwamnatin Najeriya ta canza tunani, ta sayar da duka matatun da ke ƙarƙashinta ga ƴan kasuwa.

Source: Facebook
A rahoton Daily Trust, masana na ganin cewa sayar da matatun zai kawo ƙarshen kashe-kashen kuɗin gwammnati wajen gyara yayin da ƴan kasuwa za su karbe ragamar aikin.
A wannna rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku abubuwan da ya kamata ku sani game da rufe matatar da shawarwarin masana da masu ruwa da tsaki a harkokin mai.
NNPCL ya sanar da rufe matatar Fatakwal
A ranar Juma’a, kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya sanar da cewa za a rufe matatar Fatakwal daga ranar Asabar domin gudanar da gyare-gyare na yau da kullum.
Wannan na zuwa ne watanni shida kacal bayan matatar ta dawo aiki kuma ta fara loda wa motoci kaya, bayan kammala aikin gyara da ya laƙume Dala biliyan 1.5.
Jami’in Hulda da Jama’a na NNPCL, Femi Soneye, ya tabbatar da cewa za a rufe matatar a cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X.
Sanarwar ta ce:
“Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) na sanar da jama’a cewa za a rufe matatar Fatakwal domin gudanar da gyara na yau da kullum. Za a fara gyaran daga ranar 24 ga Mayu, 2025.
Me ya kamata a sani game da matatar?
Bayan matatar ta ci gaba da aiki a Nuwamba 2024, wasu sun nuna shakku kan sahihancin lamarin inda wasu ke cewa ba duka matatar ke aiki ba, wani bangare nw kawai.
NNPCL ya dage cewa matatar Fatakwal da aka sani tana sarrafa ganga 60,000 a rana tana aiki yadda ya kamata, kuma ana ci gaba da lodin kaya, sabanin yadda ake zargi a wasu wurare.
An fara rufe matatar mai ta Fatakwal ne a watan Maris, 2019, domin yin gyara lokacin da gwamnati ta ba kamfanin kasar Italiya, Maire Tecnimont, kwangilar aikin.
Matatar Fatakwal na ɗaya daga cikin matatu huɗu da kamfanin NNPCL ke gudanarwa, kuma sun laƙume biliyoyin Daloli wajen gyara, sauran su ne matatun Kaduna da Warri.
Wannan gyaran da aka yi a matatar PHRC ya lashe aƙalla Dala biliyan 1.5, yayin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da kashe kudade kan matatun mai da ba sa aiki yadda ya kamata.
Martanin masana kan batun sayar da matatun
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa muhawarar kan sayar da matatun mai mallakar gwamnati ta jima tana gudana a Najeriya.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya taɓa sayar da su ga wasu ‘yan kasuwa masu zaman kansu da Alhaji Aliko Dangote ke jagoranta a farashin Dala miliyan 750.
Amma bayan zuwan marigayi Shugaba Umar Musa Yar’Adua, gwamnatinsa ta mayar da kudin ga ƴan kasuwar tare da soke yarjejeniyar sayar da matatun.

Source: Twitter
Nnaemeka Obiaraeri, wani masani a harkar zuba jari, ya ce gwamnati na salwantar dukiyar ƙasa wajen kashe makudan kudi a gyara matatun amma sun gaza tashi.
A cewarsa, matakin da Obasanjo ya ɗauka na sayar da matatun a 2007 shi ne mafi dacewa, kuma bai kamata a sake dowo da su hannun gwamnati ba.
"Mun kashe biliyoyin Daloli da tiriliyoyin Naira tun daga 1999 a ƙoƙarin gyara matatun nan amma babu wani abin a zo a gani.
Obasanjo ne kawai ya ɗauki sahihin mataki lokacin da ya sayar da matatun ga su Dangote, Otedola da sauran manyan ‘yan kasuwa," in ji shi.
Ya kara da cewa Naira tiriliyan 4 aka lalata a ƙarƙashin shugabannin baya na NNPCL wajen kokarin farfado da matatun.
A cewarsa, ya kamata a rufe Matatar Kaduna gaba ɗaya, a maida ta rumbun ajiya domin bututun iskar gas da ke zuwa wurin ya lalace.
Sannan ya ce matatun Warri da Fatakwal za su zama masu jawo hankalin masu saka jari, idan aka sayar da su.
'Rufe matatar Fatakwal abin kunya ne'
A nasa bangaren, tsohon sakataren ƙungiyar dillalan mai (IPMAN), Mike Osatuyi, ya bayyana cewa rufe matatar Fatakwal wani abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya.
A wata hira da aka yi da shi, Osatuyi ya ce ya kamata kamfanin NNPC ya fito fili ya bayyana gaskiyar dalilin da ya sa aka rufe matatar, kamar yadda Bussiness Day ta kawo.
“Wannan wani abin kunya ne. Muna ganin kamar matata ta dawo sabuwa da aka gyara, ba mu zata za a rufe ta haka da wuri ba," in ji shi.

Source: Twitter
A cewarsa, kudaden da aka kashe wajen gyaran matatar sun ishi gwamnati ta gina sababbin matatu guda biyu, musamman a lokacin da Naira ke da ƙima sosai.
Ya kara da cewa zuwan Matatar Dangote da ke Ibeju-Lekki a jihar Lagos, shi ne abin da ya ceci ƴan Najeriya.
PETROAN ta soki rufe matatar Fatakwal
Ƙungiyar masu gidajen sayar da mai a Najeriya (PETROAN), ta bayyana cewa rashin kwarewa ne da rashin gaskiya suka janyo rufe matatar, duk da kashe dala biliyan 1.5 a gyaranta.
A rahoton Vanguard, shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce:
“Rufe matatar Fatakwal ba komai ba ne face rashin gogewar shugabannin da ke kula da matatar. Tun farko, ba gaskiya suka faɗa game da gyaranta ba."
Ƙungiyar dillalan mai a yankin matatar Fatakwal ta fito da sanarwa mai ɗauke da gargadi, inda ta ce akwai wata "mummunar manufa" da aka ɓoye a shirin rufe matatar.
Ɗangote zai ci gaba da rage farashin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa matatar attajirin ɗan kasuwar nan, Aliko Ɗangote ta ce za ta ci gaba da rage farashin fetur duk da hauhawar farashin danyen mai.
Matatar Ɗangote ta jaddada cewa tana da niyyar ci gaba da samar da mai da araha kuma mai inganci ga ƴan Najeriya.
Hakan dai na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban jami’in hulɗa da jama’a na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina ya fitar a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng




