China Ta Hango Tarin Arziki a Najeriya, Ta Fara Gina Manyan Kamfanoni 2 a Arewa

China Ta Hango Tarin Arziki a Najeriya, Ta Fara Gina Manyan Kamfanoni 2 a Arewa

  • Gwamna Abdullahi Sule ya ce China na sha’awar lithium na Najeriya saboda tana kallon kasar a matsayin jagorar kasuwancin Africa
  • Ya ce Najeriya na da fiye da mutane miliyan 220 da GDP kusan $480bn, hakan ya sa China ke kallonta a matsayin abokiyar kasuwanci
  • Gwamnan ya kara da cewa kamfanonin lithium za su samar da ayyukan yi a Nasarawa, wanda zai habaka tattalin arzikin jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana dalilin da ya sa kasar Chine ke nuna sha'awar lithium na Najeriya.

A cewar gwamnan, China na son hakowa, sarrafawa da kasuwancin Lithium na Najeriya ne saboda tana kallon kasar a matsayin jagora a kasuwar Yammacin Afirka.

Gwamnan Nasarawa ya fadi dalilin da ya sa China ke son harkar Lithium da Najeriya
Gwamnan Abdullahi Sule | Hoton wani kamfanin sarrafa Lithium da ake ginawa a Nasarawa. Hoto: @NasarawaGovt
Source: Twitter

Dalilin China na sha'awar lithium din Najeriya

Gwamna Abdullahi ya shaidawa Channels TV cewa, kamfanin kasar Sin na gina cibiyoyi biyu na hakowa da sarrafa lithium a jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi magana yayin da aka hana shi shiga Saudiyya aikin Hajji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da ake tattaunawa da shi a cikin shirin 'Siyasar ranar Lahadi,' mai girma Abdullahi Sule ya ce:

“Yanzu haka kasar Sin na cikin juyin juya halin makamashi mai tsafta. Wannan ne dalilin da ya sa suka shirya zuba biliyoyin daloli a Afirka, kuma daga cikin kasashen Afirka, sun mayar da hankali ne kan Najeriya.
“Duk da tarin sukar da ake yi, sun mayar da hankali kan Najeriya. Meyasa? Saboda suna kallon Najeriya a matsayin jagora a kasuwar Yammacin Afirka."

- Gwamna Abdullahi Sule.

Akwai sinadarin lithium mai yawa a Nasarawa

Ya kara da cewa:

“Fiye da mutane miliyan 220, da jimillar mutanen Yammacin Afirka kusan miliyan 400, da kuma GDP da ke kusa da $480bn, suna kallon Najeriya a matsayin abokiyar kasuwanci mafi cancanta"

Yayin da wasu ke ganin zamanin man fetur, wanda shi ne babbar hanyar samun kudin shiga na Najeriya, na kusa karewa, Gwamna Abdullahi ya bayyana cewa lithium da ke da dumbin yawa a Nasarawa da wasu sassan Najeriya zai iya maye gurbin man fetur.

Kara karanta wannan

Su wanene ke juya akalar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu? Minista ya koro bayani

Gwamnan jihar na Nasarawa ya tabbatar da cewa:

“Da zarar an cire siyasa daga lamarin kuma a bar masu zuba jari su yanke shawara yadda ya kamata, to Najeriya na kan hanyar samun gagarumin ci gaba.
Gwamna Abdullahi ya ce 'yan Nasarawa za su samu ayyuka idan kamfanonin China suka fara hako lithium
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule. Hoto: @NasarawaGovt
Source: UGC

Tasirin kamfanonin lithium a Nasarawa

Ya kara da cewa:

“Wannan wani irin man fetur ne na daban da muka same shi a kasarmu. Allah ya yi wa Najeriya wannan ni’ima, kuma wannan ita ce hanyar da ya kamata mu bi."

Gwamnan ya kara da cewa kamfanonin lithium za su samar da ayyukan yi ga mazauna jihar, duk da cewa yawansu ba zai kai na bangaren noma ba.

Sai dai ya ce kwarewar da ma’aikata za su samu a wadannan kamfanoni za ta taimaka matuka wajen habaka ci gaban jihar da tattalin arzikin kasa baki daya.

Akalar Najeriya da China

Kasashen China da Najeriya na da dangantaka ta dogon lokaci a fannin kasuwanci, tattalin arziki, da zuba jari.

Tun bayan da Najeriya ta fara bude kofa ga kasashen waje a fannin zuba jari, China ta kasance daya daga cikin manyan abokan huldar Najeriya, musamman a fannoni irin su gina ababen more rayuwa, masana’antu, da hakar ma’adinai.

Kara karanta wannan

An fara raba tallafin gwamnatin Tinubu, mutane miliyan 15 za su ci gajiyar shirin

A ‘yan shekarun nan, kasar China ta kara karfafa zumunta da Najeriya ta hanyar zuba jari a manyan ayyuka kamar layin dogo, tashoshin wutar lantarki, da masana'antun sarrafa albarkatun kasa.

Sabbin hannayen jarin China a Najeriya

Daya daga cikin sabbin abubuwan da suka ja hankalin China shi ne sinadarin lithium, wanda Najeriya ke da shi sosai musamman a jihar Nasarawa.

Wannan sinadari na da matukar muhimmanci wajen kera batir na motocin lantarki da sauran kayayyakin zamani.

Bayan bukatar sinadarin lithium, China na kallon Najeriya a matsayin babbar kasuwa a Yammacin Afirka saboda yawan jama’arta da kasuwarta mai fadi.

Zuba jari daga China na taimakawa wajen samar da ayyukan yi, kara kudaden shiga, da bunkasa fasaha a cikin gida.

Wannan hulda na da alfanun gaske ga tattalin arzikin Najeriya idan aka tafiyar da ita cikin gaskiya da adalci.

China na gina Kamfanin $200m a Nasarawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kai ziyara zuwa hedikwatar kamfanin Jiuling Lithium a kasar China.

Kamfanin Jiuling Lithium zai kafa katafariyar masana’anta a Nasarawa da za ta sarrafa tan miliyan shida na lithium a cikin watanni 18, tare da samar da dubban guraben aiki.

Haka zalika, wani kamfani mai suna Canmax Lithium ya yi alkawarin biyan albashin da ya haura mafi karancin albashi na N70,000, inda ya kai har N500,000 ga wasu ma’aikata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com