Makiyaya Dauke da Makamai Sun Harbe Malamin Addini a Makurdi, Sun Sace Mutane 2
- 'Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun yi wa malamin cocin Katolika, Solomon Atongu kwanton bauna a hanyar Makurdi–Naka
- An ce miyagun sun harbe faston nan take yayin da yake kan hanyarsa zuwa Naka, suka sace mutum biyu da ke cikin motarsa
- Jami’an tsaro sun samu nasarar ceto malamin bayan ya zubar da jini mai yawa, inda aka garzaya da shi asibiti don ceto rayuwarsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue — An ruwaito cewa 'yan bindiga sun harbe wani faston Katolika da ke malinta a Cocin St. John Quasi Parish da ke Jimba, a jihar Benue.
Rahotannin sun bayyana cewa, 'yan bindigar da ake zargin makiyaya ne sun harbe Rev. Fr. Solomon Atongu, a kan hanyar Makurdi zuwa Naka.

Source: Getty Images
Makiyaya sun harbe fasto a Makurdi
An harbe faston ne da yammacin Asabar yayin da yake komawa Naka daga Makurdi, inda ya fada cikin tarkon da makiyayan suka dana masa, inji rahoton Vanguard.
Rahotanni sun ce an sace wasu mutane biyu da ke cikin motar faston, kuma an tafi da su cikin daji bayan 'yan bindigar sun dauka cewa faston ya mutu.
Wata majiya ta bayyana cewa:
“Cikin nasara, jami’an tsaro sun iso wurin da lamarin ya faru kafin faston ya mutu, sun yin gaggawar tafiya da shi asibiti a lokacin da suka fahimci ya zubar da jini mai yawa. Yanzu haka likitoci na kokarin ceto rayuwarsa."
Shugaban Katolika ya nemi addu'ar mabiyansa
A wata wasika da ya aika ga dukkanin malaman majami'u da mabiya addinin Katolika a karamar hukumar, magatakardan shugaban na Katolika a Makurdi, Rev. Fr. Shima Ukpanya, ya bukaci a taya faston da addu’a domin samun sauki cikin gaggawa.
Wani bangare na wasikar na cewa:
“Na rubuto da sunan Bishop na Diocese Katolika Makurdi, Most Rev. Wilfred Chikpa Anagbe, don nema daya daga cikin fastocinmu addu'a, Rev. Fr. Solomon Atongu.
“Ana zargin makiyaya ne suka kai masa hari ne da yammacin yau (Asabar) a yankin Tyolaha, kan hanyar Makurdi zuwa Naka, karamar hukumar Gwer ta Yamma.
“Muna fatan za mu dage da addu’a, mu roki Allah ya ba shi sauki yayin da likitoci ke kokarin ceto rayuwarsa. Allah ya karbi rokon mu, alfarmar mahaifiyar Yesu mai ceto.”
Sai dai ba a samu damar jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue, CSP Catherine Anene, ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Source: Original
An taba kashe fastoci 2 a 2018
A wani martani, wani mazaunin Jimba da ya bukaci a sakaya sunansa, ya la’anci harin, yana mai cewa hare-hare sun ya yi yawa a yankin, inda ya roki gwamnati da ta kara kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya bayyana cewa harin ya faru ne daidai ranar da ake taron makokin shekara-shekara na birne wasu fastoci biyu da aka kashe a 2018, watau Rev. Fr. Joseph Gor da Felix Tyolaha.
An ce an kashe su ne a Ayar Mbalom, karamar hukumar Gwer ta Gabas, ranar 24 ga Afrilu, 2018, kuma an binne su a ranar 24 ga Mayu.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Benue
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Benue, suka kashe mutane akalla takwas tare da jikkata wasu da dama.
Yankin Tombo, wanda ke fama da rikicin tsaro na tsawon sama da shekaru 20, ya sake shiga halin kunci, lamarin da ya tilasta wa dubban mazauna kauyukan yin hijira daga gidajensu.
Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar, CSP Catherine Anene, ta tabbatar da harin, tana mai bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


