Da duminsa: An samu Fastoci biyu sun kafa sabuwar kungiyar Boko Haram

Da duminsa: An samu Fastoci biyu sun kafa sabuwar kungiyar Boko Haram

- Wata sabuwa, wasu fastoci sun fara da'awar Boko Haram a jihar Kwara

- An samu nasarar kama biyu cikinsu kuma an gurfanar da su a kotu

- Irin haka rikicin Boko Haram ya fara a Maiduguri shekara 11 da suka gabata

An damke wasu fastoci biyu, Olumide Peter da Jasulayomi Adetola, kan laifin sauya tunanin mabiyansu domin watsi da iyayensu tare da kona takardun karatunsu saboda Boko Haramun ne.

An gurfanar da su ne a kotun majistaren Ilori ranar Alhamis inda aka cajesu da laifin yaudara, tsorata mutane, boye mutane da kuma damfara.

Alkalin kotun, Ibrahim Dasuki, ya bada umurin garkame Fastocin biyu gidan kason Oke-Kura dake Ilori, Vanguard ta ruwaito.

Bayan haka, ya dage karar zuwa ranan 28 ga Junairu, 2020.

Lauyan hukumar NSCDC, Ajide Kehinde, ya ce an ceci mutane shida da Fastocin sukayi garkuwa da su.

Ya ce Fastocin biyu masu jagorantar cocin Evidence of Christ Fellowship International Church, Agbo-Oba, Ilorin, sun ce Boko Haramun ne kuma duka takardan da mutum ya samu ta Boko, haramun ne.

Lauyan ya ce Fastocin sun kasance suna amsan kudi daga hannun kungiyoyin kasashen waje da sunan taimakawa yan gudun hijra.

Ya ce bincike ya nuna cewa Fastocin suna wa'azin cewa Boko Haramin ne kuma mabiyansu su san laifi ne karatun Boko.

Amma Fastocin sun ki amincewa da laifukan da ake zarginsu da shi.

KU DUBA NAN: Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7

Da duminsa: An samu Fastoci biyu sun kafa sabuwar kungiyar Boko Haram
Da duminsa: An samu Fastoci biyu sun kafa sabuwar kungiyar Boko Haram
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun rabawa talakawa sama da 75,000 kudi N1.5bn a jihar Kebbi, Ministar Jinkai Sadiya Farouq

A wani labarin kuwa, wata kotun Baricho dake Kirinyaga Kenya ta yanke wa wani Fasto da ya lalata yaransa mata biyu kuma yayi musu juna biyu hukuncin daurin shekaru 140 a gidan kaso.

Faston dan shekara 51 mai suna John Gichini ya gurfana gaban kotun Majistaren ne ranar alhamis kuma Alkali Anthony Mwicigi ya yanke masa hukuncin shekaru 70 kan kowace yarinya.

Amma Alkalin ya ce zai ci zaman shekarun a lokaci guda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel