Tun kafin Barin Mulki, Gwamna Sule Ya Fadi Abubuwan da ke Sanya Shi Cizon Yatsa

Tun kafin Barin Mulki, Gwamna Sule Ya Fadi Abubuwan da ke Sanya Shi Cizon Yatsa

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi tsokaci kan shekaru kusan shida da ya kwashe a ofis yana mulki
  • Abdullahi Sule ya bayyana cewa a cikin waɗannan shekarun ya gudanar da ayyukan da jama'a suke yabonsu saboda su
  • Sai dai, ya nuna cewa duk da haka akwai ayyukan da suke sanya shi cizon yatsa saboda har ya bar mulki ba za su kammalu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi magana kan babbar nadamar da yake da ita a mulkinsa.

Gwamna Sule ya bayyana cewa duk da yabon da yake samu daga jama’a kan ci gaban da ya kawo a faɗin jihar, akwai abubuwan da yake cizon yatsa a kansu saboda rashin aiwatar da su.

Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Sule ya ce ya so kammala wasu ayyuka kafin barin ofis Hoto: Abdullahi A. Sule
Source: Facebook

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin wani taro da kungiyar A.A. Sule Gida Gida ta shirya a Lafia domin bikin cikarsa shekaru shida a kan mulki, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Duk da gargaɗin Tinubu ga masu sauya sheƙa, ɗan majalisa ya tattara kayansa zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanne abubuwa ke sa Sule cizon yatsa?

Da yake jawabi a wajen ya bayyana cewa ko da yake gwamnatinsa ta samu manyan nasarori, ya so a ce wasu muhimman ayyuka sun yi nisa sosai.

Daga cikin manyan nasarorin da ya jero akwai biyan albashi a kan lokaci, biyan hakkokin ƴan fansho da suka daɗe, ci gaba a ɓangaren tattalin arziƙi da bunƙasa aikin noma.

Sai dai Gwamna Sule ya bayyana takaici game da dakatar da aikin haƙo man fetur a yankin Obi, wanda aka fara shekaru uku da suka wuce.

"Da na fi so a ce an kammala mataki na farko, na biyu da kuma na uku na aikin haƙo man fetur a Ebenyi da Obi, wanda aka fara amma yanzu kamfanin NNPCL ya dakatar."

- Gwamna Abdullahi Sule

Ya bayyana cewa burinsa shi ne ganin aikin haƙo man ya kai matakin gwaji, shigowar masu zuba hannun jari, da kuma kafa ƙaramar matatar mai.

Kara karanta wannan

Kano: An cafke matasa da ke bidiyo domin 'trending' a kusa da gidan gwamnati

Gwamnan ya ce hakan zai ba Nasarawa damar cin moriyar kaso 13% na kuɗaɗen man fetur kafin ƙarshen wa’adinsa a 2027.

Gwamna Sule ya so kafa babbar masana'anta

Gwamnan ya kuma taɓo wani gagarumin buri na kafa masana’antar haɗa motoci masu amfani da lantarki a cikin jihar.

Ya bayyana wannan aikin a matsayin ɗaya daga cikin manyan burikansa, wanda aka goyi baya da dokar da ta tilasta masu zuba jari su sarrafa kayayyakin da ake buƙata a cikin gida.

Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Sule ya ce bai ciyo bashi ba Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook
“Mun kammala mataki na farko, wato samar da sinadarin lithium. Mataki na gaba shi ne sarrafa sinadarin zuwa batir, sannan a haɗa motocin lantarki."
"Idan wannan buri bai samu ci gaba ba a hannun wanda zai gaje ni, to hakan zai ci gaba da zama abin damuwa a gare ni."

- Gwamna Abdullahi Sule

Duk da waɗannan kalubale, Gwamna Sule ya nuna jin daɗinsa kan cewa dukkan ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar, an yi su ne da kuɗin da ake da su, ba tare da an cibashi ba.

Gwamna Sule ya musanta shirin takara a 2027

Kara karanta wannan

"Arewa ba ta adawa da Tinubu," Tsohon minista ya yi magana kan 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa zai yi takarar sanata a 2027.

Gwamna Sule ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin rahotannin da ke cewa zai so ya zama sanata bayan ya sauka daga mulki.

Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa yana samun kiraye-kiraye daga ƙungiyoyi daban-daban domin ya fito takara a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng