'An Yi Abin da Ya Dace': Sanusi II kan Dawowa Sarauta, Ya Yi Wa Abba Kabir Alkawari
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana godiyarsa ga Allah da Gwamna Abba Kabir bisa dawowa kujerar sarautar da aka tsige shi
- Ya soki gwamnatin da ta shude kan kirkirar sababbin masarautu da ya ce ya saba da tarihi da tsarin da iyaye da kakanni suka gada
- Sanusi ya roki Allah ya kara hada kan gidansu, ya dawo da zaman lafiya, arziki da damina mai albarka a jihar Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana yayin bikin cika shekara daya a sarautar jihar.
Basaraken ya bayyana jin dadinsa game da samun damar dawowa kujerar da aka cire shi a shekarar 2020.

Source: Facebook
Sanusi II ya yi wa Allah godiya
Hakan na cikin wani bidiyo da shafin Sanusi Snippets ya wallafa a X a daren jiya Asabar 24 ga watan Mayun 2025.

Kara karanta wannan
Duk da gargaɗin Tinubu ga masu sauya sheƙa, ɗan majalisa ya tattara kayansa zuwa APC
A cikin bidiyon, Sanusi II ya yi godiya na musamman ga Gwamna Abba Kabir bisa sake ba shi dama.
Sarkin ya kuma soki gwamnatin da ta shude kan kirkirar masarautu wanda ya saba tarin da ake bi tun iyaye da kakanni.
A bidiyon Sanusu II ya ce:
"Dole mu godewa Allah saboda rokonsa muka yi raba masarautarmu da aka yi ya kawo wadanda za su warware, idan alkairi ne Allah ya dawo da mu kuma ya masa mana.
"Watakila mun manta ba mu roke shi idan aka dawo da mu ka da a yi rigima ba, abin da muka roke shi ya bamu, amma mun gode masa kuma dole mu yi farin ciki.
"Wannan kasa tamu da tarihi da aka kacancana wanda shi ne yafi muhimmanci a kan kujerar sarauta amma tarihi na shekaru dubu a tashi rana daya a raba kan alumma wanna shi ne babban illa.

Kara karanta wannan
Bidiyon Sanusi II da mataimakin gwamna yayin addu'ar cika shekara 1 a sarautar Kano
"Saboda haka mu na godiya ga Allah da ya warware da gode masa yau shekara daya ba a yi tashin hankali ba.
"A kasar nan an raba masarautu da yawa, a Gombe, sarakuna na san wajen guda 20 ne, jihar Zamfara suna wajen guda 19, yadda aka tasarwa raba Kano watakila sai a nan gaba a ce za a samu sarakuna 30 zuwa 40."

Source: Twitter
Sanusi II ya godewa Abba Kabir
Basaraken ya yabo na musamman ga gwamnatin Kano inda ya ce a madadin kansa dole ya yi godiya kan abin da aka yi.
Ya ce karfi na Allah ne babu abin da zai faru inda ya roki Allah ya kawo karshen dukan wata damuwa da sabani.
Ya kara da cewa:
"Tun da aka yi haka, ba a samu gwamnati da ta jajirce ta ce an yi abin da bai kamata ba, za a koma a yi gyara sai wannan gwamnati.
"Tilas a yaba musu, saboda matakin da suka dauka, har mutanen cewa suke yi sai an busa kaho, sai mahadi ya zo."
Sanusi II ya yi addu'ar Allah ya hada kan gidansu ya dawowa Kano da arzikinta da kuma damina mai albarka.
Sarki Sanusi II ya ziyarci Amurka
Kun ji cewa Sarki, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara birnin Houston da ke Texas a kasar Amurka inda ya hadu da tsofaffin abokansa.
Muhammadu Sanusi II ya ziyarci cibiyar sararin samaniya ta NASA tare da sauran ‘yan kungiyar tsofaffin daliban makarantar da suka yi a Lagos.
Sanusi II ya halarci liyafar da aka shirya musu da dare a Houston tare da fitattun mutane ciki har da Sanata Bukola Saraki da Dr Oluyinka Olutoye.
Asali: Legit.ng
