Niger: Dubun Basarake Ta Cika, an Cafke Sarki kan Zargin Taimakawa Ta'addanci
- Rundunar ƴan sanda a jihar Niger ta cafke wani basarake da wasu mutum 13 bisa zargin taimakawa 'yan bindiga a Mashegu
- An kama su ne a ranar 23 ga Mayu yayin wani samame da jami'an tsaro suka kai sansanonin 'yan bindiga a Guiwa da Telle
- An gano babura huɗu, harsashi, da shanu 10 a gidan dagacin, yayin da bincike ke cigaba don gano sauran masu hannu a ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Wani basarake ya shiga hannun jami'an tsaro bayan zarginsa da taimakawa yan bindiga a jihar Niger.
Jami’an tsaron a sun kama dagacin Guiwa da wasu mutum 13 bisa zargin taimaka wa ‘yan bindiga a karamar hukumar Mashegu.

Source: Original
Zarge-zargen da ake yi wa Sarki a Niger
Majiyoyi na leƙen asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa an kama su ne a ranar 23 ga Mayu, 2025.

Kara karanta wannan
Sojoji sun farmaki 'dan ta'adda Kachalla Murtala, sun ruguza sansaninsa a Katsina
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi suka ce an yi nasarar kama basaraken ne yayin wani samame na hadin gwiwar jami'an tsaro a yankin.
Jami’an ‘yan sanda, masu farauta da ‘yan banga suka kai samamen a sansanonin ‘yan bindiga dake kauyukan Guiwa da Telle cikin yankin.
An kama dagacin, Mai Anguwa Garba Mohammed bisa zargin ba da mafaka da kayan aiki ga ‘yan bindiga a yankin.
Jerin waɗanda aka kama. Niger
Sauran da aka kama sun fito daga kauyuka daban-daban da ake zargin suna da alaka da ‘yan bindigan da ke addabar jama’a.
Mutanen sun hada da Alhaji Abdullahi Shehu na Wawa, Umar Abubakar na Gwajibo, da Musa Mohammed daga Telle, da sauransu.
Haka kuma akwai Mohammed Abubakar na Dukku, Molema Aliyu na Pallagi, Oro Abubakar daga Arera da Shehu Alhaji Ardo daga Adogon Mallam.
Sai kuma Umar Abdullahi, Ibrahim Abubakar, Saidu Mohammed da Babuga Abdullahi, duk daga Lumma, da Mohamadu Bako daga Gwajibo.
An kuma kama Babuga Saidu daga Lumma yayin wannan samame da jami’an tsaro suka gudanar cikin kwararan bayanan leƙen asiri.

Source: Facebook
Abubuwan da aka samu a gidan Sarkin
A gidan dagacin, jami’an tsaro sun gano babura huɗu, harsashi ɗaya da shanu 10 da ake zargin ‘yan bindiga ne suka sace.
An yanka wasu daga cikin shanun uku da suka ji rauni domin kaucewa wahala bisa umarnin likitan dabbobi da ke cikin tawagar.
Majiyoyin ‘yan sanda a jihar Niger sun ce ana ci gaba da bincike kuma za su ci gaba da bankado duk masu taimaka wa ‘yan ta’adda.
Gwamna Bago ya fadi silar matsalar tsaro
Kun ji cewa Gwamna Umaru Bago na jihar Niger ya bayyana cewa talauci da jahilci ne tushen matsalar tsaron da ke addabar al'umma a Najeriya.
Bago ya bukaci a ɗauki matakai da gaggawa domin ilimantar da jama'a da fitar da su daga ƙangin talauci da kuncin da suke ciki.
Gwamnan ya faɗi haka ne da ya karɓi bakuncin tawagar masu karatun kwas din harkokin leken asiri waɗanda ke rangadi a jihar.
Asali: Legit.ng
