Sarkin Musulmi Ya Yabi Tinubu da Kirista Ya Gina Makarantar Islamiyya ga Marayu
- Sultan na Sokoto ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan yadda yake karfafa zaman lafiya tsakanin addinai, yana cewa hakan ya haifar da ci gaban tattalin arziki
- Sultan ya ce nada Tosin Ajayi, Kirista, a matsayin shugaban DSS da kuma gina makarantar addini ta Musulunci don marayu, abin koyi ne da ya dace
- Shugaban DSS ya bayyana cewa ilimi na rage rashin jin dadi, kuma hakan na taimakawa wajen magance ta da zaune tsaye da inganta tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sarkin Musulmi, Muhammed Sa’ad Abubakar III, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu a bangaren addini.
Sultan ya yabi Tinubu ne bisa kokarinsa na karfafa zaman lafiya tsakanin addinai a Najeriya.

Source: Facebook
Bangaren addini: Sultan ya yabawa Tinubu
Sarkin ya yi wannan yabo ne jiya yayin bude cibiyar koyar da addinin Musulunci ta Bola Ahmed Tinubu Darul’Ilm da shugaban DSS, Tosin Ajayi ya gina a Kaduna, cewar The Nation.
Sarkin ya shawarci ‘yan Najeriya da su kau da bambance-bambancen addini da kabila, yana mai cewa hakan ne ya kai wasu kasashe ga ci gaba.
Ya yabawa Tinubu saboda nada Ajayi a matsayin shugaban DSS, yana cewa hakan ya taimaka wajen gina dankon zumunci a sassa daban-daban na kasa.
Sarkin ya bayyana cewa Ajayi, wanda Kirista ne, ya gina makarantar Musulunci ga marayu da talakawa, lamarin da ya kira aikin da zai dawwama.
Ya ce:
“Hadewar mutane mabambantan addinai da kabilu zai taimaka wajen kawar da rabuwar kai da matsalolin da kasar ke fuskanta.
“Zuwan shugabannin hukumomin tsaro daban-daban yau yana nuna hadin kai da amincewar da suke da ita ga Tosin Ajayi."

Source: Facebook
Shugaban DSS ya fadi dalilin gina makarantar
Shugaban DSS, ta bakin tsohon daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Zalmar, ya ce ya fara tunanin gina makarantar ne tun lokacin da yake aiki a jihar.
Ya ce dokar kafa DSS na ba da dama don dakile barazanar tsaron cikin gida guda biyar, ciki har da leken asiri da ta’addanci da tayar da fitina.
A matsayinsa na jami’in tsaro, ya ce ya gano cewa rage rashin jin dadi a tsakanin jama’a hanya ce mai kyau ta dakile tayar da fitina, cewar Daily Post.
Ya kara da cewa ya gano ilimi a matsayin hanya mai amfani wajen rage rashin jin dadi da hana yaduwar rashin tsaro a cikin al’umma.
“Na gina makarantar zamani mai kyau tare da hadin gwiwar abokai da abokan aiki domin cika muradin Shugaba Tinubu.
“Wannan na daga cikin manufofina na inganta tsarin tsaron cikin gida ta hanyar hanyoyi na gargajiya da kuma sabbin dabaru."
- Cewar Zalmar
Sarkin Musulmi ya ba shawarci kan matsalar lantarki
Mun ba ku labarin cewa Sarkin Musulmi ya taɓo batun matsalar wutar lantarkin da ake fana da ita a Najeriya ta tsawon shekaru.
Sultan ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta kammala aikin madatsar ruwan Kashimbila.
Sarkin Musulmin ya nuna cewa kammala aikin zai taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar lantarki a Najeriya.
Asali: Legit.ng

