Taraba: Dangote Ya Yi Alkawarin Zuba Jari a Arewa bayan Taron Habaka Tattali
- Aliko Dangote da Tony Elumelu sun yi alkawarin zuba jari a jihar Taraba, musamman a bangarorin noma da kuma makamashi
- Sun bayyana hakan ne yayin taron Taravest da aka gudanar a Jalingo, inda suka yabawa kyakkyawan yanayin kasuwanci na jihar
- Manya da dama sun halarci taron, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima da Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Shahararrun ‘yan kasuwa Alhaji Aliko Dangote da Tony Elumelu sun bayyana shirinsu na zuba jari a jihar Taraba, musamman a bangarorin noma da makamashi.
Rahotanni sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin karfafa tattalin arzikin jihar da kuma ciyar da Najeriya gaba.

Source: Facebook
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya wallafa a X cewa shugaba Bola Tinubu ya yaba da yadda aka shirya taron.
A yayin taron, Dangote da Elumelu sun jaddada cewa dole ne a fara karfafa hannun jarin cikin gida kafin a iya jawo masu zuba jari na ƙetare su zo su sa kudinsu a Najeriya.
Dangote: "A tallafa wa masu zuba jari na gida"
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa masu zuba jari daga ƙetare ba za su zo ba matuƙar ba su ga cewa na cikin gida na ci gaba da bunkasa ba.
Ya ce gwamnati na da muhimmiyar rawa wajen tallafa wa masu zuba jari na gida domin jawo wasu daga waje.
Ya kara da cewa Taraba na da yalwar albarkatu da dama da za a iya amfani da su wajen habaka tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Elumelu: "Zuba jari zai magance yunwa da talauci"
Shugaban Transcorp Group, Tony Elumelu, ya ce shirinsu na zuba jari a Taraba ya haɗa da hada kai da bankin UBA da kuma gidauniyarsa ta taimakon matasa.

Kara karanta wannan
El Rufai ya faɗi minista 1 da za su bari a muƙaminsa bayan sun tura Tinubu Legas a 2027
Punch ta wallafa cewa Tony Elumelu ya ce:
"Zuba jari yana samar da ayyukan yi, yana rage yunwa da talauci, kuma yana ƙarfafa zaman lafiya."
Shettima ya yaba da taron tattali a Taraba
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen taron, ya bayyana Taraba a matsayin “babbar cibiyar noma ta Najeriya.”
Kashim Shettima ya ce jihar na da muhimmiyar damar samar da wutar lantarki ta hanyar ruwan Mambila.
Shettima ya ce taron yana da matuƙar muhimmanci wajen shirya Najeriya don fuskantar karuwar jama'a da bukatun tattalin arziki na gaba.

Source: Twitter
Gwamnoni, Sarkin Musulmi sun yabi taron Taraba
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, wanda ya wakilci kungiyar gwamnonin Najeriya, ya bayyana cewa Taraba na da fifiko a harkar noma, kuma daidai ne a zuba jari a bangaren.
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yabawa Gwamna Agbu Kefas bisa yadda jihar ta zauna lafiya cikin shekaru biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan
Shettima, Atiku, Sarkin Musulmi, Dangote, manyan Najeriya na taron tattali a Taraba
Dangote zai cigaba da rage kudin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta bayyana cewa 'yan Najeriya za su cigaba da samun saukin man fetur.
Aliko Dangote ya bayyana cewa zai cigaba da kokari wajen rage wa 'yan Najeriya kudin mai domin saukaka musu rayuwa.
Ya bayyana haka ne yayin da ya ke yabawa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan cigaba da sayar masa da danyen mai da Naira.
Asali: Legit.ng
