Gwamnatin Tinubu za Ta Rabawa Gidajen Talakawa Miliyan 2.3 Tallafin Kudi
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da aikin tantance shirin raba tallafi domin tabbatar da cewa masu bukata kadai ke cin gajiyar shirin
- A cewar NIMC, gidaje miliyan 2.3 aka riga aka tantance kuma za a fara biyan su tallafin rage radadin sauye-sauyen tattalin arziki da aka kawo
- Bankin Duniya ya nuna damuwa kan jinkirin aiwatar da shirin duk da riga an fitar da dala miliyan 530 cikin bashin da aka amince da shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fara tantance mutane a wani bangare na kokarin da take yi na gyara shirin bayar da tallafin kudi ga ‘yan kasa masu bukata.
Hakan na zuwa ne bayan koke-koken da ake yi kan rashin ganin sauyin da shirin tallafin ke haifarwa, musamman tun bayan cire tallafin man fetur da karya darajar Naira a 2023.

Kara karanta wannan
BUA ya yi maganar saukar farashin abinci da siminti bayan ganin Tinubu a Aso Villa

Source: Facebook
Jaridar Business Day ta wallafa cewa shugabar hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC), Abisoye Coker-Odusote ta ce an riga an tantance gidaje miliyan 2.3 a karkashin shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abisoye Coker-Odusote ta bayyana cewa wadanda aka tantancen za su fara karbar kudin tallafin nan ba da jimawa ba.
Yadda ake tantance masu karbar tallafi
Coker-Odusote ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a hedikwatar NIMC da ke Abuja, inda ta ce ana gudanar da aikin ne a karkashin shirin NSSN.
Ta ce:
"A halin yanzu muna tantance mutanen da ke cikin rajistar tallafi domin a tabbatar da cewa an kai kudin ga wadanda suka dace.
"Mun riga mun tantance mutum miliyan 2.3 kuma za mu fara biyan su ba da dadewa ba."
Ta jaddada cewa tantancewa da tabbatar da sahihancin bayanan dan kasa na da matukar muhimmanci don kauce wa biyan wadanda ba su cancanta ba.
Bankin duniya ya nuna damuwa kan tallafi
A sabon rahoton shekarar 2025 da bankin duniya ya fitar, an bayyana cewa daga cikin gidaje miliyan 15 da aka yi niyya, gidaje miliyan 5.6 kacal ne suka karbi wani kaso na tallafin.
Bankin ya ce hakan ya faru ne sakamakon rashin tabbatar da sahihancin bayanan wadanda ke cikin rajistar, inda ya bukaci gwamnati ta kara azama wajen taimaka wa masu rauni.
Rahoton ya kara da cewa samun sahihiyar shaidar zama dan kasa ta hanyar amfani da bayanan yatsa da hoton fuska na da matukar tasiri wajen fadada shirin.
Martanin Tinubu ga bankin duniya kan tallafi
A wata hira da aka yi da mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki, Tope Fasua, ya ce jinkirin ya faru ne saboda bukatar tabbatar da gaskiya da sahihanci a tsarin.
Tashar Arise News ta rahoto ya ce:
“Mun fi son bi a hankali da tabbatar da cewa kudin ya kai ga wadanda suka dace fiye da gaggawa da fadawa hadarin zamba.”

Source: Facebook
An fara raba tallafin kudi a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Dikko Umaru Radda ta fara raba tallafin kudi ga talakawa masu bukata a ihar Katsina.
Gwamna Dikko Umaru Radda da kansa ya kaddamar da shirin, inda ya ce hakan zai rage radadin rayuwa ga al'umma.
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar wa manema labarai cewa duk wanda aka tantance a cikin shirin zai samu N75,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

