Rivers: Tinubu Ya Ji Wuta, Ya Roki Kotun Koli kan Shari'arsa da Gwamnonin PDP

Rivers: Tinubu Ya Ji Wuta, Ya Roki Kotun Koli kan Shari'arsa da Gwamnonin PDP

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kotun koli ta yi watsi da karar gwamnonin PDP da ke kalubalantar dokar ta baci da dakatar da Simi Fubara
  • Lauyan gwamnatin Najeriya ya ce kotun koli ba ta da hurumin sauraron karar, domin ba ta shafi rikici tsakanin jihohi da tarayya kai tsaye ba
  • Jihohin PDP sun roƙi kotun ta soke dakatarwar da kuma nadin shugaban riko, suna masu cewa matakin ya saba wa kundin tsarin mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana da gwamnonin PDP suka maka shi a kotu kan dokar ta-ɓaci a Rivers.

Tinubu ya nemi kotun koli ta yi watsi da karar gwamnonin PDP da ke ƙalubalantar dakatarwar da aka yi a Jihar Rivers.

Tinubu ya roki kotun koli kan shari'arsa da gwamnonin PDP
Tinubu ya roki gwamnonin PDP su janye kararsa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, PDP Governor's Forum.
Source: Twitter

Yadda gwamnonin PDP suka kai karar Tinubu

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu da EFCC kan yin shiru bayan kama Gudaji Kazaure

Premium Times ta ce ganin wannan mataki ya fusata wasu jihohi 11 inda suka garzaya kotun koli don ƙalubalantar dokar da shugaban ƙasa ya ɗauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin sun hada da Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Delta, Enugu, Osun, Oyo, Plateau, Taraba da Zamfara.

Jihohi 7 ne suka fara kai karar a watan Maris, amma daga baya suka kai 11, kowanne ta bakin kwamishinan shari’arsa.

Shin Tinubu ya samu korafin kai tsaye?

Ba a kai wa shugaban ƙasa ƙara kai tsaye ba, sai dai ta hannun Ministan Shari’a na Tarayya, Lateef Fagbemi.

Majalisar Tarayya, wacce ta amince da dokar ta baci da dakatar da Gwamna Fubara, ita ce ke matsayin wanda ake kara na biyu.

A takardar ƙin yarda da karar da Ministan Shari’a ya gabatar a ranar 9 ga Mayu, ya ce kotu ba ta da hurumi.

Fagbemi ya ce jihohin ba su bayyana wani rikici tsakaninsu da Tarayya ba, ko wani hakki da aka karya.

Ya ce:

“Don haka muna roƙon kotun koli ta yi watsi da karar nan gaba ɗaya."

Kara karanta wannan

Alƙawarin da Ganduje ya yi bayan sanatoci 3 sun yi fatali da jam'iyyunsu zuwa APC

Tinubu ya roki kotu kan shari'arsa da gwamnonin PDP
Tinubu ya roki kotun koli ta kori karar gwamnonin PDP. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tinubu ya fadi dalilin dakatar da Fubara

Mai taimakawa Shugaban Ƙasa kan Shari’a, Taiye Hussain Oloyede, ya tabbatar da cewa an dakatar da Fubara ne saboda rikici da ‘yan majalisa.

Ya ce rikicin siyasa da harin da ake kai wa kadarorin mai ya haddasa matsalar tsaro, wanda ya sa aka ayyana dokar ta baci.

Ya ce Majalisar Tarayya na da hurumin amincewa da dokar, kuma ba dole ne su kirga kuri’u ɗaya bayan ɗaya ba.

Oloyede ya ce gwamnonin sun shigar da kara ne saboda fargabar cewa Tinubu zai iya ayyana dokar ta baci a jihohinsu.

Rivers: Gwamna ya zame hannunsa a karar Tinubu

Kun ji cewa gwamnonin PDP sun gamu da cikas a ƙarar da suka shigar gaban kotun ƙoli suna ƙalubalantar ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya koma APC kwanan nan, ya janye kan shi daga ƙarar.

Oborevwori ya ce tun da ya bar PDP, babu dalilin da zai sa ya ci gaba da zama a ɓangaren waɗanda ke ƙalubalantar Bola Tinunu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.