Tinubu Ya Ji Dadin Ganin Ayyukan Gwamna, Ya Nemi a Ba Shi Fili Ya Gina Gida a Jihar
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana aiki kafada da kafada da Gwamna Charles Soludo domin ciyar da jihar Anambra
- Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta farko zuwa jihar tun bayan da ya karbi ragamar jagorancin Najeriya
- Shugaban ya bayyana jin dadinsa da ci gaban jihar, har ya bayyana burinsa na samun fili domin gina gidan ritaya a Anambra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Anambra – Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana aiki kafada da kafada da gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, domin ci gaban jihar.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin ziyararsa ta farko a Anambra tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2023.

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa a yayin ziyarar, Tinubu ya kaddamar da gine-ginen gwamnati da dama da suka hada da sabon gidan gwamnatin jihar Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ganawarsa da magoya baya a filin taro na Alex Ekwueme, Tinubu ya jinjinawa Soludo bisa gina kyakkyawan tubali ga ci gaban jihar.
Bola Tinubu ya yabi gwamnan Anambra
Premium Times ta ce Tinubu na ganin ayyukan gine-ginen da ake yi a jihar sun yi daidai da hangen nesa na Soludo na mayar da Anambra ta zama Dubai, Taiwan da kuma Silicon Valley a nahiyar Afrika.
Tinubu ya ce:
“Na kaddamar da muhimman ayyuka guda biyu, wato Solution Fun City da sabon gidan gwamnatin jihar, a matsayin matakin farko wajen mayar da Anambra a ‘African Dubai-Taiwan-Silicon Valley (ADTS)’.
“Tare da sauye-sauyen da ake samu a fannin gine-gine da bunkasa jarin dan Adam, wannan babbar alama ce ta hangen nesa da irin abin da shugabanci nagari ke iya cimmawa a kankanin lokaci.”
Yadda Anambra ta sauya ya burge Tinubu
Shugaban kasa Tinubu ya bayyana jin dadinsa da irin ci gaban da aka samu a jihar, inda cikin raha ya bukaci Soludo da ya samo masa fili domin gina gidansa na ritaya a jihar.

Source: Facebook
Ya ce:
“’Yan shekarun baya Dubai daji ce kawai. Amma yau ta zama cibiyar duniya saboda namijin kokarin mutum daya da ya yarda. Na tuna lokacin da Soludo ke so ya hade bankunan Najeriya, mutane da dama sun ce ba zai yiwu ba.
“Anambra na da dimbin albarkatu, kuma tare da Soludo, za mu iya hada kai wajen hanzarta aiwatar da hangen nesan nan.”
“Ina mai tabbatar da cewa daga yanzu ba kawai abota ce a tsakaninmu ba, ni cikakken dan asalin Anambra ne yanzu! Wata kila Soludo, abokina kuma gwamnanku, zai nemo min fili in gina gidan ritaya bayan na kammala hidimar kasa.”
Gwamnan Anambra ya goyi bayan tazarcen Tinubu
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnan Anambra, Charles Soludo, ya ce jam’iyyarsa ta APGA ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Soludo ya fadi haka a yayin ziyarar Tinubu a jihar Anambra ranar Alhamis, a wurin taron da aka gudanar a filin Alex Ekwueme da ke birnin Awka, tare da alkawarin aiki tare da cimma burinsu.
Wannan na zuwa ne yayin da dangantakar siyasa tsakanin Tinubu da Soludo ke kara karfi, inda shugaban kasar ya bayyana kansa a matsayin dan asalin Anambra kuma abokin gwamnan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


