Bauchi: Bayan Kisan Mutane 25, Gwamna Ya Fadi Yankin da Ƴan Ta'adda Suka Mamaye
- Gwamna Bala Mohammed ya nuna damuwa kan sake bullar 'yan bindiga a dajin Alkaleri, yana mai kira ga sojojin sama su fatattake su
- A bikin haɗin kan sojoji da fararen hula, gwamnan ya yabawa sojojin sama, sannan ya yi Allah wadai da kisan 'yan banga a Alkaleri
- Rahoto ya nuna cewa an kwashe awa daya ana dauki ba dadi tsakanin 'yan bindiga da 'yan bangar, inda a karshe aka kashe mutane 25
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwarsa game da sake bullar 'yan bindiga a dajin Alkaleri, inda ya ce sun karɓe ikon yankin.
Gwamnan ya yi kira ga sojojin saman Najeriya da su haɗa kai da sauran hukumomin tsaro don tsabtace yankin da kuma fatattakar 'yan bindigar.

Source: Facebook
An yi bikin hadin kan sojoji da fararen hula
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen bikin 'Ranar Haɗin Kan Sojoji da Fararen Hula' ta 2025 a hedikwatar sojojin sama da ke Bauchi, kamar yadda AIT News ta ruwaito.
Abubuwan da suka gudana a bikin sun hada da nuna takardun tarihi na sojojin sama, tattaunawar aiki da kuma nuna nau'ukan kayan aikin sojojin sama daban-daban.
An yi taron ne da nufin zaburar da ɗaliban da aka gayyata da kuma nuna masu wasu muhimman nasarorin da sojojin saman Najeriya suka samu.
Gwamna Mohammed wanda ya kasance babban baƙo a taron, ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan tsaro, Ahmed Abdulrahman.
Gwamna ya yi Allah wadai da kisan mafarauta
Bala ya yabawa sojojin saman Najeriya bisa muhimman nasarorin da suka samu kafin daga bisani ya jawo hankalinsu game da sake bayyanar 'yan bindiga a Dajin Alkaleri.
Ko kafin wannan taron, gwamnan jihar na Bauchi ya yi Allah wadai da kisan 'yan banga da 'yan bindiga suka yi a ƙauyen Mansur, da ke karamar hukumar Alkaleri.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin ya faru ne a lokacin da ƙwararrun mafarauta da 'yan banga ke sintiri na yau da kullum a yankunan Duguri, Mansur da Dajin Mada.

Source: Facebook
Yadda aka kashe mutane 25 a dajin Bauchi
Ana zargin cewa 'yan bindiga sun yi wa mafarauta da 'yan bandar kwanton bauta a safiyar 4 ga Mayu, 2025, lamarin ya ya jawo musayar wuta mai zafi.
An ce bayan fafatawa ta kusan awa daya, an kashe 'yan banga tara yayin da mutane 11 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su suka mutu.
A cikin wata sanarwa da Mukhtar Gidado ya fitar a ranar Litinin, Gwamna Bala ya nuna matuƙar baƙin ciki game da kisan 'yan sa kan tare da mika ta'aziyya.
Gwamna Bala ya ba al'ummar Bauchi tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta kawo karshen barazanar 'yan ta'adda.
Bauchi: 'Yan sanda sun gwabza da 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Bauchi ta yi nasarar kashe 'yan bindiga biyu a wani samame da ta kai dajin Madan.
A yayin wannan samame da aka gudanar a yankin Gwana bayan gwabza fada, an samu nasarar ƙwato bindiga kirar AK-49 tare da harsasai tara.
Rundunar 'yan sandan ta sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da yaƙi da 'yan bindiga a jihar Bauchi tare da buƙatar haɗin kan al'umma domin inganta tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


